Babaji

5702 Posts

Bayanan sirrin sun nuna DSS ta ankarar da Hedikwatar Tsaro wata guda kafin harin Yelwata

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Wasu bayani na sirri sun nuna cewa Hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS) ta yi aiken saƙo ga Moses Gara, wanda shi ne Kwamandan Atisayen Whirl Stroke (OPWS) game da wani shiryayyen hari a ƙauyukan Jihohin Benuwai da Nasarawa a watan Mayu. A shekara 2018 ne Hedikwatar Tsaro (DHQ) ta ƙaddamar da atisayen, wanda ya ƙunshi jami'an sojoji, ƴan sanda da na DSS. A ranar 13 ga watan Yuni ne ƴan bindiga suka farmaki al'umma a Ƙauyen Yelwata dake Ƙaramar Hukumar Guma a jihar Benuwai, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane sama da…
Read More

SDP ta dakatar da shugabanta, Shehu Gabam da wasu bisa badaƙalar kuɗaɗe

Daga BELLO A. BABAJI Jam'iyyar SDP ta sanar da dakatar da Shugabanta na Ƙasa, Shehu Gabam bisa zargin sa da hannu a sauya akalar wasu kuɗaɗen jam'iyyar. Haka kuma, ta dakatar da Odita na ƙasa, Nnamdi Clarkson da Shugaban matasa, Chukwuma Uchechukwu. Sakatarenta na yaɗa labarai, Araba Aiyenigba ya bayyana hakan a wata takarda, ranar Talata. Ya ce, an ɗauki matakin ne saboda samun su da hannu dumu-dumu a yin harƙallar kuɗaɗe da dama, da azurta kawunansu da sauya akalar kuɗaɗe ba tare da amincewar kwamitin ayyuka ba. Sanarwar ta kuma ce, Shehu Gabam ya miƙa takardar bayanan kuɗaɗe da…
Read More

Gwamnonin PDP za su gana da INEC kan rikicin kwamitin majalisar zartarwar jam’iyyar

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Yayin da rikicin cikin gida a jam'iyyar PDP ke cigaba da ta'azzara da rikicin muƙamin sakatare na ƙasa da na zaman kwamitin majalisar zartarwarta, gwamnonin jam'iyyar za su gana da Hukumar zaɓe (INEC) a Abuja, ranar Talata. A sanarwar da INEC ta fitar ta hannun Sakatarenta na riƙon ƙwarya, Halliru Aminu, za a gudanar da zaman ne a yau da misalin ƙarfe 2 na rana, a ɗakin taro na hukumar zaɓen. Majiya daga jam'iyyar da dama sun bayyana cewa, a yayin taron ne za a tattauna akan batun muƙamin Sakataren. Haka kuma, gwamnoni da…
Read More

Isra’ila ta amince da tsagaita wuta da Iran

Isra'ila ta tabbatar tare da amincewa da shiga yarjejeniyar tsagaita wuta da Iran a yaƙin da suke gwabzawa a tsakaninsu. Isra'ila ta ce, ta amince da tsagaitawar ne bayan "ta cimma burinta," na ƙaddamar da yaƙin a Iran tun a farko. A wata sanarwa da ta fitar, Isra'ila ta ce ta daƙile "dukkan barazanar" da take fuskanta daga Iran na mallakar nukiliya da makamai masu linzami. Sanarwar ta kuma ƙara da cewa ta "samu nasarar kawo tsaiko a tsarin shugabancin sojin Iran, da ma tarwatsa gomman kadarorin gwamnatin Iran masu muhimmanci." Ta ƙara da cewa, hare-harenta sun "tarwatsa dakarun Basij…
Read More

Tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Iran ta fara aiki, inji Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Iran ta fara aiki. Sai dai shugaban ya yi kira ga bangarorin biyu su mutunta yarjejeniyar Donald Trump ya sanar da tsagaita buɗe wuta tsakanin Isra'ila da Iran a ranar Litinin da dare a shafinsa na sada zumunta. Trump ya ce, Iran za ta fara aiwatar da tsagaita wutar, daga baya kuma Isra'ila za ta dakatar da kai wa Iran hari. Isra'ila dai ta ci gaba da kai hare-hare cikin Iran, kamar yadda ministan tsaronta ya bayyana, yayin da kuma Iran ta yi gargaɗi ga mazauna birnin Ramat…
Read More

Babu barazana a Abuja duk da gargaɗin hukumomin tsaron Amurka – Gwamnatin Tarayya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Tarayya ta ce babu barazanar tsaro a birnin tarayya Abuja ga al'umma. Gwamnatin ta bayyana haka ne a ranar Litinin bayan da hukumomin Amurka a Nijeriya suka gargaɗi baki ɗaya ƴan Amurka da su ƙaurace wa dukkan sansanin sojoji da ofisoshin gwamnati a birnin. A sanarwar da hukumar US Mission Nigeria ta fitar, ta yi kira ga ma'aikatan ofishinta na jakadanci da iyalansu da su ƙaurace wa wuraren sojoji da gine-ginen gwamnati musamman waɗanda ake gudanar da taruka. Akan haka ne gwamnatin Nijeriya ta ofishin Ministan Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris,…
Read More

Iran ta kai wa sansanin sojin Amurka hari a Ƙatar da Iraƙi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Iran ta ce ta kai hare-haren makamai masu linzami a sansanin sojojin Amurka, lamarin da ƙasar ta kira da martani mafi girma da nasara kan hare-haren Amurka a cikin ƙasar. Kamfanin dillancin labaran ƙasar na Tasnim ya ce, dakarun juyin juya halin ƙasar sun ƙaddamar da hare-haren makamai masu linzami kan sansanin sojin Amurka dake Ƙatar da Iraƙi A sa'o'in da suka gabata ne aka samu labaran jin ƙarar abubuwan fashewar a Ƙatar. Saidai a yayin tsokaci game da hakan, Amurka ta ce adadin makamai masu linzami da ta yi amfani da su wajen…
Read More

MOPPAN ta yi ta’aziyyar rasuwar mahaifin Rahama Sadau

Daga BELLO A. BABAJI Ƙungiyar Masu Shirya Fina-finai ta Ƙasa (MOPPAN) ta miƙa saƙon ta'aziyyarta ga jarumar fina-finan Kannywood, Nollywood da kuma Bollywood, wato Rahama Sadau bisa rasuwar mahaifinta. A sanarwar da ta fitar ta hannun Kakakinta, Ibrahim Amarawa, MOPPAN ta ce tana taya jarumar da ɗaukacin iyalanta da makusantanta jimamin babban rashin da aka yi musu. Ta kuma ce, mahaifin nata ya yi rayuwa mai cike da ababen koyi ga ƴan baya duba da yadda ya kasance mai hikima kuma mai kirki wajen mu'amala. MOPPAN ta yi fatan Allah ya ba su haƙurin juriyan rashin mamacin, wanda rayuwarsa ta…
Read More

Tinubu ya nemi a kafa jami’an ko-ta-kwana na ECOWAS yayin miƙa jagoranci ga Bio na Sierra Leone

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Tinubu ya miƙa ragamar jagorancin ECOWAS ga Shugaba Julius Maada Bio na ƙasar Sierra Leone, bayan kammala shekaru biyunsa a yayin taron ƙungiyar karo na 67, ranar Lahadi. Gabannin haka ne aka samu raɗe-raɗen cewa akwai yiwuwar Bassirou Faye na Senegal ya gaje shi a kujerar. A watan Yulin 2023 aka zaɓi Tinubu a matsayin shugaban ECOWAS, inda kuma aka sake zaɓar sa shekara guda bayan haka a Abuja. Tinubu ya samu ƙalubalen dawo da martabar dimukraɗiyya a shiyyar Afirka ta Yamma a lokacin da ƙasashen Nijar da Mali da Burkina Faso…
Read More

Sabon shugaban ECOWAS ya yi kira ga haɗin kai da ci-gaba bayan kama aiki

Sabon shugaban ECOWAS ya yi kira ga haɗin kai bayan kama aiki Daga BELLO A. BABAJI Shugaba Bio na Sierra Leone, wanda shi ne sabon shugaban Kungiyar ƙasashe masu Tattalin Arziƙi na Yammacin Afirka (ECOWAS) ya nemi ƙasashen da ke ƙarƙashin jagorancin ƙungiyar da su haɗe kawunansu domin cimma nasarori a fannonin da suka saka a gaba. Ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karɓi ragamar jagorancin ƙungiyar a ranar Lahadi a Fadar Shugaban Ƙasa dake Abuja, bayan wa'adin Shugaban Bola Tinubu na biyu ya ƙare. Ya ce, zai mayar da hankali kan ƙalubale da damanmaki da suke da…
Read More