23
Jun
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Biyo bayan jira na sama da shekaru 20 tsofaffin ma'aikatan kamfanin 'Nigeria Airways' da aka rushe za su karɓi fanshonsu, yayin da Ministan Sufurin Jiragen Sama da Ci-gaban Sararin Samaniya, Festus Keyamo ya amince da biyansu haƙƙoƙin nasu. Lamarin da ya zama gagarumar nasara a tarihin harkar sufurin jiragen sama na Nijeriya tun bayan rufe kamfanin a ranar 30 ga watan Satumbar 2004. Da dama daga cikin ma'aikatan sun rasu, yayin da masu rai acikinsu suke rayuwa a halin ƙunci wajen jiran a yi musu adalci da biyansu kuɗaɗensu. An sanar da amincewar ne…
