Babaji

5702 Posts

Kano: Bom ɗin sojoji ya halaka mutane biyar da raunata wasu da dama

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Mutane biyar sun rasu a yayin da wani abin fashewa da aka yi zargin na jami'an sojoji ne ya tarwatse a Kano. Haka kuma wasu guda 15 sun samu munanan raunuka. Rahotanni sun bayyana cewa, al'amarin ya auku ne a safiyar ranar Asabar, inda tuni jami'an tsaro da na bada agajin gaggawa suka garzaya wajen da abin ya faru. Kwamishinan ƴan sandan jihar, Ibrahim Adamu Bakori, wanda ya ziyarci wajen jim-kaďan da faruwar al'amarin, ya ce ta yiwu bom ɗin a ƙarƙashin ikon sojoji ya ke wanda aka gaza kula da shi yadda ya…
Read More

Mutumin da ya tunkari Tinubu a Kaduna yana da taɓin hankali, inji ƴan sanda

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rundunar ƴan sanda a Kaduna, ta ce mutumin da ya yi ƙoƙarin kutse a tsakanin jami'an tsaro a lokacin da Shugaba Bola Tinubu ke ƙaddamar da wasu ayyuka a jihar, an haifi shi ne da larurar rashin lafiyar ƙwaƙwalwa. Kakakin rundunar, DSP Mansir Hassan a wata takarda, ya ce sunan mutumin shi ne Umar Mohammed, wanda mazauni ne na Unguwar Mu'azu a Kaduna. Ya bayyana cewa, an tantance mutumin ne a matsayin ɗan jam'iyyar APC ɗauke da wasu alamu da ke tabbatar da haka ciki har da hotunan Tinubu da Gwamna Uba Sani, lamarin…
Read More

2027: Haɗakar Atiku da El-Rufa’i na neman INEC ta yi musu rijistar sabuwar jam’iyya

Daga BELLO A. BABAJI Ƙungiyar ƴan ɓangaren adawa ta Ƙasa a ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasiru El-Rufa'i, ta yi aiken takardar neman yi wa sabuwar jam'iyya rajista ga Hukumar Zaɓe (INEC). Sunan jam'iyyar shine ADA, wato 'All Democratic Alliance'. An rubuta takardar ne a ranar 19 ga watan Yuni, inda kuma ta je gaban INEC a washe-gari, lamarin da ke nuna haɗakar ta fi gamsuwa da shi akan haɗewa da wata jam'iyya. Daga cikin waɗanda suka goyi bayan samar da jam'iyyar akwai tsohon gwamnan Jihar Ribas, Rotimi Amaechi da Umar Arɗo, wanda…
Read More

Yaƙin Isra’ila da Iran: ‘Yan Nijeriya a Iran sun koka bayan jami’an ofishin jakadanci sun tsere

Daga BELLO A. BABAJI Wasu ƴan Nijeriya a Tehran, Babban Birnin Iran, sun shiga mawuyacin hali tare da kokawa bayan da jami'an ofishin jakadancin Nijeriya a ƙasar suka bar su kara-zube a yayin da rikici tsakanin ƙasar da Isra'ila ke ƙara ta'azzara. Kwanaki takwas kenan ana fafatawa tsakanin Isra'ila da Iran, wanda aka fara a lokacin da Isra'ilar ta farmaki ma'ajiyar makaman nukiliyar Iran, lamarin da ya yi sanadiyyar rasa rayukan manyan sojoji da masana kimiyya. Bayan Iran ta mayar da martani cikin gaggawa, ɗaruruwan mutane sun rasa rayukansu a yayin da wasu da dama suke jinya, wanda a sanadiyyar…
Read More

Kisan Yelwata: Mazauna ne suka yaudari dakarunmu gabannin harin, inji Babban Hafsan Tsaro

Daga BELLO A. BABAJI Babban Hafsan Tsaron Nijeriya (CDS), Janar Christopher Musa ya bayyana cewa dakarun sojoji suna garin Yelwata a Jihar Benuwai ranar 13 ga watan Yuni, 2025, inda aka yaudare su da wani rahoton kai hari na ƙarya daga wani gari dake kusa da yankin, lamarin da ya sa maharan suka yi nasarar hallaka mutane da dama. Janar Musa ya faɗi hakan ne a yayin hira da manema labarai a Abuja, ranar Alhamis. Ya ce, a saboda yaɗa batun kai harin na ƙarya a garin dake kusa ya sa sojoji suka mayar da hankali tare da zuwa wajen…
Read More

Kwastomomin bankuna sun yi ƙorafin cajis sama da kima ga CBN

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙungiyar Kwastomomin Bankunan Nijeriya (BCAN) ta ce ta aika saƙon ƙorafi ga Babban Bankin Nijeriya game da yawan cajis da ake cirewa a asusun kwastomomi. Shugaban BCAN, Uju Ogubunka ya bayyana hakan a ranar Alhamis, a yayin taron fasahar AI da aka shirya da nufin inganta ayyukanta da gamsar da kwastomomi kan harkokin kuɗaɗe a Abuja. An ɗauki matakin ne a yayin da bankuna suke cazar kwastomomi kuɗaɗen da babu su a cikin waɗanda CBN ya amince da su a hukumance. A lokacin da ya ke jawabi a taron, Ogubunka ya ce sun rubuta…
Read More

2027: Sai bayan babban taron APC Tinubu zai zaɓi abokin tafiya, inji Fadar Shugaban Ƙasa

Daga BELLO A. BABAJI A yayin babban taron jam'iyyar APC na shekarar 2026 ne Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai zaɓi abokin tafiyarsa a babban zaɓen 2027 da ke tafe. Kakakin Shugaban Ƙasa, Bayo Onanuga ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin ganawa da manema labarai a Abuja. Ya ce, sai an ayyana ɗan takara a hukumance daga jam'iyya kafin a yi maganar zaɓar wanda zai zame masa mataimaki, inda ya ce ba a tare ake faɗar su ba. Onanuga ya kuma ce, irin haka ne ya faru a lokacin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a lokacinda ya nemi tsayawa takara…
Read More

Abuja: ‘Yan sanda sun fara binciken bidiyon gawar macen da aka samu ɗaure a otal

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rundunar ƴan sanda a Abuja, ta ƙaddamar da bincike akan wani faifan bidiyo da ya karaɗe kafafen watsa labarai, wanda ke nuna yadda aka wata mata an ɗaure mata hannaye ta baya a wani ɗakin otal a yankin Gwarimpa dake birnin tarayya. Kakakin rundunar, SP Josephine Adeh ta bayyana hakan a wata takarda, ranar Laraba, inda ta ce hukumar ta samu labarin yaɗuwar bidiyon wanda ake cecekuce akansa. Ta ce, tuni aka baza jami'ai zuwa wajen da ake zargin faruwar al'amarin a ƙarƙashin kwamishinan ƴan sandan Abuja, Ajao S. Adewale, wanda ya umarci a…
Read More

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Namadi Sambo ya ƙaryata batun koma wa APC

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Namadi Sambo, ya yi watsi da rahoton da ke cewa ya koma jam'iyya mai mulki ta APC. A sanarwar da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Umar Sani ya fitar, Namadi ya bayyana hakan a matsayin abinda aka ƙirƙira da nufin ruɗar da al'umma. Sanarwar ta kuma ce, hoton da ake yaɗawa a jikin labarin, wanda aka gan shi tare da Gwamna Uba Sani na Kaduna kuma da ke ƙoƙarin gaskata labarin, an yi shi ne tun da jimawa. Haka kuma, sanarwar ta jaddada cewa, tsohon mataimakin shugaban…
Read More

Mele Kyari ya shiga tsaka-mai-wuya bayan Majalisar Dattawa ta bai wa NNPCL mako guda ya bada ba’asin tiriliyan N210 da suka ɓata

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Majalisar Dattawa ta bada wa'adin mako guda ga Babban Kamfanin Man Fetur na Ƙasa ya gabatar da bayani dalla-dalla game da ɓatar wasu maƙudan kuɗaɗe da adadinsu ya kai kimanin sama da tiriliyan N210 daga rahoton bayanan kuɗaɗe tun daga shekarar 2017 zuwa 2023. Kwamitin Majalisar akan kuɗaɗen al'umma, wanda ya yi nazari akan rahotannin kamfanin ya bada umarnin, bayan nuna damuwa akan wasu kuɗaɗe da aka kashe da waɗanda suka shigo ba tare da yin gamsassun bayanai akansu ba. Ana ganin hakan zai jefa Mele Kyari cikin matsala duba da cewa shi ne…
Read More