Babaji

5702 Posts

Gwamnoni, Ministan Tsaro da NSA sun yi taron gaggawa kan matsalolin tsaro

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnoni daga jihohin Nijeriya sun taru a Abuja inda suke gudanar da zaman gaggawa game ta'azzara da lamarin taɓarɓarewar tsaro ke yi. An yi taron ne a ƙarƙashin Ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya (NGF) a sakatariyarta dake Abuja, wanda ya samu halartar gwamnoni da mataimakan gwamnoni daga jihohi 36 na ƙasar. Duk da cewa ba a bayyana asalin abinda aka a tattauna a taron ba, ganin Mai bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkar Tsaro, Nuhu Ribaɗu da Ministan Tsaro, Badaru Abubakar, ya nuna cewa matsalolin tsaro ne aka gina tattaunawar a kai. Hakan na zuwa…
Read More

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Namadi Sambo ya koma APC

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Laraba ne tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Namadi Sambo ya fice daga Jam'iyyar PDP zuwa mai mulki, wato APC. Hakan na ƙunshe a wani rubutu da ɗaya cikin ƴan gaba-dai-gaba-dai na APC mai suna Imran Muhammad ya wallafa ta shafin X a Jihar Kaduna. Ana ganin Namadi Sambo ya yanke shawarar sauya sheƙa ne duba da rikicin cikin gida da ya dabaibaye PDP a mataki na jihohi da ma ƙasa baki ɗaya. Gwamna Uba Sani na Kaduna, shi ne wanda ya karɓi Sambo bayan sauya sheƙar tasa a Gidan Gwamnatin jihar, ranar Laraba.…
Read More

Tinubu ya umarci jami’an tsaro su kamo masu hannu a kashe-kashen Benuwai

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarnin gaggawa ga Sufeto Janar na Ƴan Sanda, Kayode Egbetokun, da Babban Hafsan Tsaro, Janar Christopher Musa, da su gaggauta kama makasan mutane sama da 100 da aka kashe a harin da wasu ƴan ta’adda suka kai a ƙauyen Yelewata na jihar Benuwe. Ya bayyana haka ne a wani taron tattaunawa da manyan shugabannin jihar da aka gudanar a gidan gwamnatin jihar Benuwe da ke Markudi. Taron ya haɗa da Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, tsoffin gwamnonin jihar, sarakunan gargajiya, da kuma gwamnonin jihohin Kwara, Imo,…
Read More

Jami’ar ABU ta haramta sanya matsatstsun kaya, shiga ta rashin mutunci da runguma a farfajiyar makaranta

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ƙoƙarinta na kare martabar addini da al'adu, Jami'ar Ahmadu Bello dake Zariya ta gabatar da sabon tsarin shiga ga ɗalibai da malamai, wanda ya hana su sanya gajerun kaya da ɗamanmu da sanya dogayen gashin gira da kuma runguma a farfajiyar makaranta. Bayanin hakan na ƙunshe a wata takarda da hukumar gudanarwar jami'ar ta fitar a ranar Litinin, inda ta ce ta yi hakan ne duba da yadda wasu ke yin shiga ta rashin mutunci, wanda a cewarta hakan ya saɓa wa doka da zamantakewar al'ummarta, don haka za a hukunta duk wanda…
Read More

Yanzu-yanzu: Shugaba Tinubu ya isa Benuwai kan kashe-kashe

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Tinubu ya isa Makurɗi, Babban Birnin Jihar Benuwai domin ziyartar mutanen Ƙauyen Yelwata dake Ƙaramar Hukumar Guma a jihar. Tinubu ya isa Filin jiragen sama dake sansanin sojojin sama na Makurɗi ne da misalin ƙarfe 12:58 na rana. Zai gana ne da muhimman masu-ruwa-da-tsaki a jihar da nufin kawo ƙarshen munanan hare-haren da suka yi sanadin mutuwar mutane da dama a sassan jihar. A saboda haka ne gwamnatin jihar ta sanar da yau Laraba a matsayin ranar hutu ga ma'aikata a jihar.
Read More

2025/2026: Manchester United za ta karɓi baƙoncin Arsenal a wasannin farko na Premier League

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar kula da gasar Premeir ta ƙasar Ingila (FA) ta fitar da jaddawalin gasar na bana, wanda za a fara ranar Juma'a, 15 ga watan Agustan 2025. Wadda ta lashe gasar a kakar da ta gabata, wato Liverpoool, za ta fara kare kambin ne a gida inda za ta haɗu da Bournemouth a ranar farko ta gasar a kakar wasa ta 2025/26. Manchester United kuwa, za ta fara gasar ne da karawa da babbar abokiyar hamayyarta, Arsenal a filin wasa na Old Trafford. Liverpool ta lashe gasar ne a kakar farko ta sabon kocin…
Read More

Iran ta jefa makamai a na’urar tsaron Isra’ila

Iran ta fara ƙaddamar da hare-haren akan wasu sassan Isra’ila a wanan karon da shu’umin makami mai linzami samfurin Fattah a cikin daren Talata wayewar safiyar Laraba a yayin da Isra’ila ta mayer da martani ta hanyar kai gagarumin farmaki a wajen birnin Teheran da cibiyoyin soji da kuma wata babar jami’a. Dakarun juyin juya hali na Iran a nasu ɓangaren, sun shaida cewa makamai masu linzamin da ƙasar ta harba sun kutsa kai ne cikin na’urar tsaron Isra’ila tare da haddasa ɓarna mai tarin yawa a wasu sassan ƙasar. Ya zuwa yanzu ƙasashen biyu ba su fitar bayanai a…
Read More

Rikicin Iran: Jamus ta jaddada goyon bayanta ga Isra’ila

Daga BELLO A. BABAJI A ranar Talata ne Babban Kansilan ƙasar Jamus, Friedeich Merz ya bayyana cikakken goyon bayansu ga Isra'ila a yaƙin ƙarfin soja da ke faruwa tsakanin Isra'ilan da Iran. Ya bayyana hakan ne a yayin hira da wata gidan jaridar ƙasar a babban taro na G7 da akq gudanar a Kanada, inda ya ce abinda Isra'ila ke yi tana yi ne a madadin dukkaninsu. Ya ce, mulkin Mullah ya yi musu illa matuƙa ta yadda an samu mace-mace da dama da lalata ga duniya. Haka kuma, kansilan ya ce hare-haren Isra'ila akan Iran ka iya haifar da…
Read More

Tinubu ya jagoranci ƙaddamar da gina sabuwar hedikwatar INEC a Abuja

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Tinubu ya jagoranci buɗe gina babban ofishin Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) a Abuja. Za a gina sabuwar Sakatariyar INEC ɗin ne a yankin Zambezi Crescent dake birnin da nufin magance matsalar faɗaɗa ofishin hukumar tun da jimawa. Ministan Abuja Nyesom Wike ne wanda ya gabatar da aikin. A lokacin da ya ke magana a yayin ƙaddamar da taron a ranar Talata, Shugaba Tinubu ya jinjina wa ministan bisa gabatar da aikin, inda ya ce hakan gagarumar gudumawa ce ga ci-gaban dimukraɗiyya tare da yi masa godiya akan haka. Haka kuma, Tinubu…
Read More

Jita-jitar ƙarya: APC ba ta da shirin sauya Shettima, inji jigo a jam’iyyar

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A yayin da ake cigaba da raɗe-raɗen cewa akwai rikici a tsakanin Shugaba Bola Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shettima, jigo a APC Ismaeel Ahmed, ya yi watsi batun, inda ya ce babu wani shiri da jam'iyyar ke yi na sauya Mataimakin Shugaban Ƙasar da wani a zaɓen 2027. A yayin hira da gidan talabijin na Channels, tsohon mamban kwamitin amitattun jam'iyyar ya bayyana zargin a matsayin jita-jita mara asali, yana mai cewa babu ƙamshim gaskiya game da rahotannin da ke nuna akwai rashin jituwa a tsakanin su. Ya ce, akwai yarda ɗari bisa ɗari…
Read More