
Daga BELLO A. BABAJI
A ranar Talata ne Babban Kansilan ƙasar Jamus, Friedeich Merz ya bayyana cikakken goyon bayansu ga Isra’ila a yaƙin ƙarfin soja da ke faruwa tsakanin Isra’ilan da Iran.
Ya bayyana hakan ne a yayin hira da wata gidan jaridar ƙasar a babban taro na G7 da akq gudanar a Kanada, inda ya ce abinda Isra’ila ke yi tana yi ne a madadin dukkaninsu.
Ya ce, mulkin Mullah ya yi musu illa matuƙa ta yadda an samu mace-mace da dama da lalata ga duniya.
Haka kuma, kansilan ya ce hare-haren Isra’ila akan Iran ka iya haifar da kawo ƙarshen jagorancin jamhuriyar Musulunci, yana mai bada misali da waɗanda aka kai wa Iran a makon da ya gabata.
Ya kuma ce, zai yi wuya a ce mulkin mullah ya koma da ƙarfinsa kamar yadda ya ke a baya duba da ɓarnar da aka yi wa jagorancin sojin Iran da dakarun juyin juya hali.
A lokacin da aka yi amsa tambaya game da ko Majalisar Ɗinkin Duniya ka iya shiga sahun masu nuna ƙiyayya kan ƙarfin sojin Iran, Merz ya ce babu wani mataki ko shiri akan haka daga gwamnatin Amurka a yanzu.
A ranar Juma’a ne Isra’ila ta kai harin ba-zata a ma’ajiyar makaman nukiliyar Iran, wanda ya yi sanadin rasa rayukan da dama daga cikin manyan sojojinta tare da wasu masana kimiyya da nufin daƙile ƙoƙarin Iran na mallakar makaman ƙare-dangi, lamarin da ya sa aka shiga musayar wuta a tsakanin ƙasashen biyu.
