Tinubu ya jagoranci ƙaddamar da gina sabuwar hedikwatar INEC a Abuja

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Tinubu ya jagoranci buɗe gina babban ofishin Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) a Abuja.

Za a gina sabuwar Sakatariyar INEC ɗin ne a yankin Zambezi Crescent dake birnin da nufin magance matsalar faɗaɗa ofishin hukumar tun da jimawa.

Ministan Abuja Nyesom Wike ne wanda ya gabatar da aikin.

A lokacin da ya ke magana a yayin ƙaddamar da taron a ranar Talata, Shugaba Tinubu ya jinjina wa ministan bisa gabatar da aikin, inda ya ce hakan gagarumar gudumawa ce ga ci-gaban dimukraɗiyya tare da yi masa godiya akan haka.

Haka kuma, Tinubu ya ce daga cikin muhimman ayyukan gwamnatinsa akwai ƙoƙarin tabbatar da gaskiya a harkokin hukumar, wanda samuwar sabuwar sakatariyar za ta taimaka wajen cimma hakan.

Ya ƙara da cewa, hakan ya nuna yadda gwamnati ke ƙoƙarin bada goyon baya ga cin gashin kan INEC da ci-gabanta wajen aiwatar da lamuran zaɓuka cikin inganci.

Da ya ke jawabi, Shugaban hukumar Farfesa Mahmood Yakubu ya jinjina wa hukumar gudanarwar birnin ƙarƙashin Wike bisa samar da ci-gaban wanda ya ce zai kawo ƙarshen matsalolin rashin wadataccen fili a yayin ayyukanta.

Ya kuma ce, a saboda rashin wadataccen fili, INEC ta karɓi hayar wurare biyu a yankin Wuse Zone II domin ma’aikata da harkokinsu.

By Babaji