Jita-jitar ƙarya: APC ba ta da shirin sauya Shettima, inji jigo a jam’iyyar

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A yayin da ake cigaba da raɗe-raɗen cewa akwai rikici a tsakanin Shugaba Bola Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shettima, jigo a APC Ismaeel Ahmed, ya yi watsi batun, inda ya ce babu wani shiri da jam’iyyar ke yi na sauya Mataimakin Shugaban Ƙasar da wani a zaɓen 2027.

A yayin hira da gidan talabijin na Channels, tsohon mamban kwamitin amitattun jam’iyyar ya bayyana zargin a matsayin jita-jita mara asali, yana mai cewa babu ƙamshim gaskiya game da rahotannin da ke nuna akwai rashin jituwa a tsakanin su.

Ya ce, akwai yarda ɗari bisa ɗari tsakanin Tinubu da Shettima don hakan bututuwan da ke nuna akwai rikici ko shirin canza Shettima da wani ba gaskiya bane.

Ahmed kuma ya yi kira ga mambobin jam’iyyar da ƴan Nijeriya da su mayar da hankali wajen nasarorin shugabanci a madadin rikicin siyasa, yana mai cewa gwamnati tana da sauran muhimman ayyuka da ta ke ƙoƙarin aiwatarwa ga al’umma.

Kalaman jigon sun biyo bayan tsaikon da aka samu ne a taron APC reshen Arewa maso Gabas da aka yi a Jihar Gombe a lokacin da Shugaban jam’iyyar a reshen, Mustapha Salihu ya ayyana sunan Tinubu a matsayin ɗan takara ba tare da haɗa shi da na Shettima ba.

Akan haka ne, tsohon mamban kwamitin amitattun ya ce hakan ba ya nuna akwai tsama ko shirin sauya mataimakin shugaban ƙasar duba da cewa abu ne da ya ke akwai shi a al’adar jam’iyyar da tsarinta.

By Babaji