
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Jihar Kano ta amince da jagorantar babban taron ƙasa akan fannin ƙirƙira domin bunƙasa tattalin arziƙin ƙasa.
Lamarin ya biyo bayan miƙa bukatar hakan ne da Gidauniyar Masana’antar Fina-finai ta Kannywood ta yi duba da rawar da jihar ta ke takawa wajen ciyar da al’adu da bunƙasa harkar ƙirƙira a Arewacin Nijeriya.
Haka kuma, taron zai zama fage na nuna dabarun inganta harkokin masana’antar fina-finai, fasahar ƙawa, waƙoƙi, rubuce-rubuce da ayyukan dijital.
A sanarwar da kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida na jihar, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya fitar a ranar Talata, ya ce taron zai haɗa masu-ruwa-da-tsaki daga sassa daban-daban na ƙasar daga ma’aikatu, hukumomi, manyan ƴan kasuwa da kuma fagagen dijital kamar su Netflix da Amazon.
Ya kuma ce, za a tattauna akan fannin ƙirƙira da yadda ya ke tasiri a harkar tattalin arziƙin ƙasa da samar da ayyukan yi da kuma bunƙasa harkokin ƙirƙira a garuruwa.
Kazalika, gwamnatin ta kirayi muhimman masu-ruwa-da-tsaki da su bada gudumawarsu wajen ganin taron ya yi nasara wajen cimma manufar da aka shirya domin shi, ta yadda za a inganta matasa, tattali da al’adun al’umma.
