Daga USMAN KAROFI
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta kammala shirye-shiryen gaggawa domin kwaso ‘yan Najeriya da suka maƙale a ƙasashen Isra’ila da Iran, sakamakon rikicin da ke ƙara tsananta tsakanin ƙasashen biyu.
Kimiebi Ebienfa, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin waje, ya fitar da wata sanarwa a daren Talata inda ya bayyana cewa ofisoshin jakadancin Najeriya a Tel Aviv da Tehran suna aiki tare da ‘yan Najeriya da abin ya shafa don tabbatar da dawowarsu cikin aminci.
Ma’aikatar ta buƙaci duk ‘yan Najeriya da ke ƙasashen da rikicin ya shafa da su kiyaye ƙa’idojin tsaro da kuma tuntuɓar ofishin jakadancin Najeriya mafi kusa da su domin rajista da samun ƙarin bayani. Gwamnati ta yaba da jajircewar ma’aikatan diplomasiyya da ke ƙasashen biyu da kuma irin haɗin gwiwar da ake yi da hukumomin cikin gida da na ƙasashen duniya don ganin an cimma nasarar fitar da ‘yan Najeriya cikin gaggawa da tsaro.
Sanarwar ta kuma ƙara da cewa gwamnatin Najeriya na nan daram kan ƙudurinta na kare rayuka da walwalar ‘yan Najeriya a gida da ƙasashen waje, tare da kira da a dakatar da rikicin nan da nan.
Gwamnati ta buƙaci ɓangarorin da rikicin ya shafa da su zauna a teburin sulhu, su mutunta dokokin kare rayukan fararen hula da su rungumi hanyoyin warware rikici ta lumana.
Rikicin ya ƙara tsananta ne bayan Isra’ila ta kai hari kan kusan wurare 100 a Iran, ciki har da sansanonin soja da cibiyoyin makamashi, lamarin da ya yi sanadin mutuwar manyan hafsoshin soja na Iran. Daga cikin waɗanda suka rasa rayukansu akwai Shugaban Hafsoshin Tsaro na Iran, Janar Mohammad Bagheri, da Kwamandan Rundunar Juyin Juya Hali, Hossein Salami. Ayatollah Khamenei, Shugaban Addini na Iran, ya bayyana harin a matsayin “yaƙin da aka ayyana”, yana mai gargaɗin cewa Isra’ila za ta ɗanɗana sakamako mai raɗaɗi.
