INEC ta ƙi amincewa da sanarwar PDP kan taron masu ruwa tsaki

Spread the love

Hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) ta yi watsi da bukatar jam’iyyar PDP na gudanar da taron kwamitin zartarwa na ƙasa (NEC) karo na 100, saboda rashin bin ƙa’idojin da doka ta shimfiɗa. INEC ta bayyana cewa sanarwar taron da PDP ta miƙa ba ta da hannu na sakataren jam’iyyar tare da na shugaban riko, kamar yadda doka ta bukata a ƙarƙashin sashe na 2(12)3 na dokokin 2022.

Sanarwar INEC wadda Hajiya Hau’ru Aminu, sakatariyar wucin gadi ta hukumar ta sa hannu a kai, ta bayyana cewa Umar Damagum kaɗai ne ya sa hannu a takardar, ba tare da haɗin gwiwar Sakatare Samuel Anyanwu ba. Hukumar ta jaddada cewa ko da yake PDP ta miƙa buƙatar a cikin wa’adin kwanaki 21, rashin cikakken sa hannu ya sa ba za ta amince da buƙatar ba.

Taron NEC da PDP ke shirin gudanarwa a ranar 30 ga Yuni a Abuja na da nufin tattauna batutuwan cikin gida da suka haɗa da rikicin shugabanci, tantance rahotannin kwamitoci da kuma amincewa da zaɓukan yankuna. Sai dai jam’iyyar na fuskantar rikicin cikin gida tun bayan zaɓen 2023, wanda ya janyo sauya sheka da dama zuwa jam’iyyar APC, ciki har da Gwamnan Jihar Delta, Sheriff Oborevwori da mataimakinsa.

A halin yanzu, wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP kamar Bode George na nuna ƙwarin gwiwa cewa za su shawo kan rikicin kafin taron NEC. A gefe guda kuma, Atiku Abubakar yana ta ƙoƙarin haɗa kan ‘yan adawa, ciki har da Peter Obi da Nasir El-Rufai, domin fuskantar APC a zaɓen 2027. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da G5 ƙarƙashin jagorancin Nyesom Wike ke matsa lamba a mika tikitin shugaban ƙasa na 2027 zuwa kudu.

By ukarofi