NUJ a Katsina ta yi bikin cika shekara 70 da kafuwa

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Ƙungiyar ‘yan jarida ta ƙasa reshen Jihar Katsina ta gudanar da bikin cika shekara 70 da kafuwa a faɗin ƙasar.

Bikin ya samu halartar manyan jami’an tsaro da malaman jami’ar FUDMA da Umar Musa Yar’adua da kuma makarantar kimiyya da fasaha ta Hassan Usman a Katsina.

Sauran sun haɗa da shugabannin kafafen yaɗa labarai na gwamnati da masu zaman kansu da na kafofin sadarwa.

Kwamishinan yaɗa labarai da al’adu Dr Salisu Bala Zango wanda ya wakilci gwamnan jihar, a jawabinsa kira yayi ga ‘yan jaridu a jihar da ko da yaushe su rinƙa bin ƙa’idojin aikin jarida kamar yadda tsarin mulkin ya tanadar.

Dikko Raɗɗa ya nuna gamsuwa da yadda ‘yan jarida ke gudanar da aikin su bisa ƙwarewa da bin dokokin ƙasa ta shimfida na harkokin da suka shafi yaɗa labarai.

Daga nan sai gwamnan yayi kira ga ‘yan jaridu da na kafofin sadarwa da su guji yaɗa labarai na ƙarya wanda yin haka na kawo koma baya ga ƙoƙarin gwamnati na kawo cigaban al’ummar da samar da abubuwan more rayuwa a jihar.

Ya ce akwai kyakkyawar haɗaka tsakanin gwamnatin jihar da kafen yaɗa labarai a jihar.

“Haka ma yasa gwamnati ta shiga yarjejeniya na yaɗa aikace-aikacen ta da gidan rediyo da wasu jaridu a jihar”, Inji Dikko Raɗɗa.

Gwamnan ya kuma yi kira ga ƴan jarida a jihar da su haɗa kai da gwamnatin jihar don Samar da zaman lafiya.

A nasa jawabin shugaban ƙungiyar yan jaridu a jihar kwamred Tukur ƊanAli Hassan ya bayyana nasarorin da ƙalubale da ƙungiyar ta samu ƙarƙashin jagorancin sa.

Ya yabawa gwamna Dikko Raɗɗa kan gudummawar da yake ba manema labarai musamman kafofin yaɗa labarai mallakan gwamnatin jihar.

Ɗan Ali yace a tsawon shekara biyar yana jagorancin ƙungiyar a duk shekara sai sun gudanar da taron ƙarawa juna sani da sauran tarurruka na cigaban ƙungiyar.

Ya yabawa ya’yan ƙungiyar kan yadda suke gudanar da aikin su bisa ƙwarewa tare da biyayya ga ƙungiyar.

Dr Sama’ila Balarabe na kwalejin kimiyya da fasaha na Hassan Usman da ke Katsina ya gabatar da ƙasida kan gudummawar da yan jaridu ke badawa ga al’umma.

By ukarofi