Gwamnatin Benuwai ta bada hutu ga ma’aikata bisa ziyarar Tinubu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Jihar Benuwai ta ayyana Laraba, 18 ga watan Yuni, 2025 a matsayin ranar hutu ga ma’aikata a sakamakon ziyarar da Shugaba Bola Tinubu zai kai wa jihar.

A sanarwar da Sakatariyarta, Serumun Deborah Aber ta fitar, ta ce shugaban ƙasar zai yi ziyarar ta’aziyya ne na kwana ɗaya domin jajenta wa gwamnatin jihar da al’ummarta bisa hare-haren da suka sabbaba rasa rayuka da dama a sassan jihar.

Ta bayyana cewa, an ɗauki matakin bada hutun ne domin bai wa ƴan jihar damar yin maraba ga Shugaba Tinubu cikin girmamawa.

Saidai, ta ce hutun bai shafi ma’aikata da ke da wajiban ayyuka akansu ba, waɗanda suka haɗa da jami’an lafiya, hukumomin tsaro da kuma cibiyoyin bankuna.

Haka kuma ana kira ga al’umma da su yi dandazo domin zuwa tarbar shugaban da ƴan tawagarsa a yayin ziyarar tasu ta musamman.

A jiya Litinin ne Shugaba Tinubu ya sauya tsarin ayyukansa domin kai ziyara jihar Benuwai kan sababbin hare-hare da aka kai wa al’umma a wasu yankunan jihar.

By Babaji