
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya (NAHCON) ta ruwaito cewa kimanin mahajjatan Nijeriya guda 6,528 ne suka dawo gida daga Saudiyya bayan kammala aikin hajjin bana.
Lamarin ya biyo bayan da jiragen gida guda 16 suka iso Nijeriya a ranar Talata, 17 ga watan Yuni.
An tsara jigilar ɗebo mahajjatan ne daga jiragen sama na Nijeriya a cigaba gudanar da aikin jigilarsu yadda ake buƙata, lamarin da ya samu taimakon masu-ruwa-da-tsaki a harkokin sufurin jiragen sama.
Ta kuma ce, ana yin hakan ne da nufin tabbatar da dawowar dubunnan mahajjatan cikin aminci bayan kammala ibadarsu a ƙasa mai tsarki.
A sanarwar da ta fitar ta kafar X, NAHCON ta bayyana cewa, tana koƙarin tabbatar da shirin ne a tsanake domin ganin ta kimtsa dawowar alhazan bisa tsari.
Haka kuma, tana sanya ido akan ayyukan cibiyar ta wadda ke Makkah, inda a halin yanzu ta ke fatan sake sako wasu jiragen nan da wasu ƴan kwanaki.
