Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Tsohon shugaban ƙasa Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana samar da ababen more rayuwa a matsayin ginshiƙin bunƙasar rayuwar al’umma da tattalin arziki da ci gaban kowace ƙasa.
Tsohon shugaban ƙasar ya bayyana haka ne a lokacin da yake ƙaddamar da titin Zanna a yankin G.R.A, wanda gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal ya sake ginawa a wani ɓangare na bikin cikar sa shekaru biyu, a Gusau babban birnin jihar a ranar Talata.
A cewarsa, kyakkyawar hanyar sadarwa, tsaro, samar da kiwon lafiya, samar da abinci, ruwa da tsaftar muhalli, sufuri da sadarwa, sune mabuɗin cigaban ɗan Adam a kowace ƙasa.
Obasanjo ya yabawa gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal bisa gagarumin ƙoƙarinsa na samar da kayayyakin more rayuwa waɗanda ke da tasiri kai tsaye ga al’ummar jihar cikin shekaru biyu da ya yi yana mulki.
“Haƙiƙa irin sauyin da aka samu ta fuskar samar da ababen more rayuwa a Jihar Zamfara a ƙarƙashin jagorancin gwamna Dauda Lawal alama ce da ke nuna cewa al’ummar jihar sun shaida yadda dimokuraɗiyya ta samu.
Tsohon shugaban ƙasar ya yi kira ga sauran gwamnonin da su yi koyi da gwamna Dauda Lawal wajen gyara jihohinsu da kayayyakin more rayuwa masu ma’ana don ci gaban jiharsu da ci gaban al’ummarsu.
Jaridar Blueprint Manhaja ta ruwaito a yayin ziyarar tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya ƙaddamar da asibitin Yariman Bakura Specialists Hospital Gusau, Kwanar Birnin Ruwa da dai sauransu.
Da yake jawabi tun da farko, gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, yace ya baiwa gwamnatinsa muhimmanci kan harkokin kiwon lafiya, tsaro, ilimi, albarkatun ruwa, gina tituna da samar da ayyukan yi a wani ɓangare na shirin ceton jihar, domin ci gaban jihar.
Gwamna Dauda Lawal ya yabawa tsohon shugaban ƙasa Obasanjo bisa girmama gayyatar da aka yi masa, inda ya ce hakan zai ƙara kawo ci gaban jihar.
