Peter Obi ya yaba wa Tinubu bisa shawarar zuwa Benuwai kan sababbin hare-hare

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ɗan takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi ya jinjina wa Shugaba Bola Tinubu bisa yanke shawarar zuwa Jihar Benuwai sakamakon kashe mutane sama da 200 a makon da ya gabata.

A ranar Litinin ne Tinubu, ta ofishin Kakakinsa, Bayo Onanuga ya sanar da soke tafiyarsa zuwa Kaduna domin kai ziyara zuwa Benuwai da nufin duba matakin ɓarnar da hare-haren ƴan ta’adda ya yi akan al’ummar jihar.

A yayin tsokaci game da hakan ne a wata takarda, Obi, wanda ke sukar tsarin shugabancin Tinubu, ya ce abin farin ciki ne ga al’umma a ce shugaban ƙasar zai ziyarci inda ake kisan gilla a Benuwai.

Ya yi godiya ga shugaban ƙasar tare da kira a gare shi da ya kuma ziyarci Jihar Neja, inda ambaliyar ruwan sama ta yi sanadin hallaka mutane da dama da ɗaiɗaita wasu a Ƙaramar Hukumar Mokwa.

Obi ya ƙara da cewa, ganin Tinubu a wuraren da ke fama da matsalolin tsaro, abu ne da zai ƙarfafa musu gwiwa da rage musu raɗaɗin ƙuncin da suke ciki.

Haka kuma, ya shawarci Shugaban ƙasar da ya ƙarfafa tsaro a sassan ƙasar musammman wuraren da ke fama da ayyukan ta’addanci.

By Babaji