Babaji

5702 Posts

Gwamnatin Kano za ta jagoranci taro akan fannin ƙirƙira

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Jihar Kano ta amince da jagorantar babban taron ƙasa akan fannin ƙirƙira domin bunƙasa tattalin arziƙin ƙasa. Lamarin ya biyo bayan miƙa bukatar hakan ne da Gidauniyar Masana'antar Fina-finai ta Kannywood ta yi duba da rawar da jihar ta ke takawa wajen ciyar da al'adu da bunƙasa harkar ƙirƙira a Arewacin Nijeriya. Haka kuma, taron zai zama fage na nuna dabarun inganta harkokin masana'antar fina-finai, fasahar ƙawa, waƙoƙi, rubuce-rubuce da ayyukan dijital. A sanarwar da kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida na jihar, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya fitar a ranar Talata,…
Read More

Gwamnatin Benuwai ta bada hutu ga ma’aikata bisa ziyarar Tinubu

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Jihar Benuwai ta ayyana Laraba, 18 ga watan Yuni, 2025 a matsayin ranar hutu ga ma'aikata a sakamakon ziyarar da Shugaba Bola Tinubu zai kai wa jihar. A sanarwar da Sakatariyarta, Serumun Deborah Aber ta fitar, ta ce shugaban ƙasar zai yi ziyarar ta'aziyya ne na kwana ɗaya domin jajenta wa gwamnatin jihar da al'ummarta bisa hare-haren da suka sabbaba rasa rayuka da dama a sassan jihar. Ta bayyana cewa, an ɗauki matakin bada hutun ne domin bai wa ƴan jihar damar yin maraba ga Shugaba Tinubu cikin girmamawa. Saidai, ta ce hutun…
Read More

Jirage 16 sun dawo da mahajjatan Nijeriya 6,528, inji NAHCON

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya (NAHCON) ta ruwaito cewa kimanin mahajjatan Nijeriya guda 6,528 ne suka dawo gida daga Saudiyya bayan kammala aikin hajjin bana. Lamarin ya biyo bayan da jiragen gida guda 16 suka iso Nijeriya a ranar Talata, 17 ga watan Yuni. An tsara jigilar ɗebo mahajjatan ne daga jiragen sama na Nijeriya a cigaba gudanar da aikin jigilarsu yadda ake buƙata, lamarin da ya samu taimakon masu-ruwa-da-tsaki a harkokin sufurin jiragen sama. Ta kuma ce, ana yin hakan ne da nufin tabbatar da dawowar dubunnan mahajjatan cikin aminci bayan kammala ibadarsu a…
Read More

Peter Obi ya yaba wa Tinubu bisa shawarar zuwa Benuwai kan sababbin hare-hare

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ɗan takarar Shugaban Ƙasa na jam'iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi ya jinjina wa Shugaba Bola Tinubu bisa yanke shawarar zuwa Jihar Benuwai sakamakon kashe mutane sama da 200 a makon da ya gabata. A ranar Litinin ne Tinubu, ta ofishin Kakakinsa, Bayo Onanuga ya sanar da soke tafiyarsa zuwa Kaduna domin kai ziyara zuwa Benuwai da nufin duba matakin ɓarnar da hare-haren ƴan ta'adda ya yi akan al'ummar jihar. A yayin tsokaci game da hakan ne a wata takarda, Obi, wanda ke sukar tsarin shugabancin Tinubu, ya ce abin farin ciki ne…
Read More

Abinda ya sa na tsame sunan Shettima yayin ambatar Tinubu – Mataimakin Shugaban APC a Arewa ta Gabas

Daga BELLO A. BABAJI Mataimakin Shugaban APC na Ƙasa a Arewa maso Gabas, Mustapha Salihu, ya bayyana dalilansa na ƙaddamar da Shugaba Bola Tinubu a matsayin ɗan takarar da zai wakilci jam'iyyar a babban zaɓen 2027 ba tare da haɗa shi Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ba, lamarin da ya nuna cewa akwai ƙamshim gaskiya a jita-jitar rikicin cikin gida a APC. Salihu, a yayin hira da gidan talabijin na Channels, ya ce rashin ambatar Tinubu tare da Shettima a taron jam'iyyar na Shiyyar Arewa maso Gabas da aka yi a Jihar Gombe ya yi daidai da tsarin babban taron…
Read More

Kotu ta yi watsi da buƙatar Gwamnatin Tarayya ta kama Natasha kan zargin ɓatanci

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A ranar Litinin ne Babbar Kotun Tarayya dake Abuja ta ƙi amincewa da buƙatar Gwamnatin Tarayya ta neman a bada izinin kama Sanatar Kogi Ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan. Hakana ya biyo bayan rashin zuwa kotu da ta yi kan zargin ɓatanci da ta yi akan wasu manyan ƴan siyasa. Mai Shari'a Muhammed Umar a yayin sauraron ƙarar, ya ce ba a gabatar wa Natasha saƙon tuhumar ba a hukumance, don haka ba lallai ba ne sai ta gurfana a kotun ba. Saboda haka ne alƙalin ya ce ba za a amince da buƙatar gwamnatin…
Read More

Yanzu-yanzu: Sufeton ƴan sanda ya je Benuwai, ya baza jami’ai domin daƙile kashe-kashe

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Sufeton ƴan sanda (IGP), Kayode Egbetokun ya je Jihar Benuwai dake Arewa ta Tsakiya, inda wasu mahara suka farmaki al'umma a ranar Juma'a da kashe da dama daga cikinsu tare da ɗaiɗaita wasu ɗaruruwa. Jihar Benuwai tana fama da matsalolin kashe-kashe na tsawon shekaru a sakamakon faɗar ƙabilanci da ke tsakanin manoma da makiyaya. Saidai, a ƴan kwanakin nan wasu mahara ne ke ƙaddamar da hare-hare a ƙauyukan dake sassan jihar. Kimanin mutane 160 ne aka kashe a makonni kaďan da suka gabata, lamarin da ya jefa al'ummar jihar halin zaman ɗar-ɗar. A ranar…
Read More

Ƙungiyar Editocin Nijeriya na shirin zaɓar sabbin jagorori yayin taronsu a Enugu

Daga BELLO A. BABAJI Ƙungiyar Manyan ƴan Jaridu ta Ƙasa, wato Nigerian Guild of Editors (NGE) za ta gudanar da babban taron mambobinta na Biennial National Convention a Enugu, daga ranar 26 zuwa 29 ga watan Yuni, 2025 mai taken 'Building a Secure and Cohesive Nigeria: The Role of Dailogue, Inclusion, and the Media'. A sanarwar da Shugaban ƙungiyar, Mista Eze Anaba da Sakatarenta, Iyobosa Uwugiaren suka fitar, NGE ta ce taron zai hada aƙalla sama da editoci guda 400 da wasu sanannun mutane. Ministan Labarai da Wayar da Kai, Ahaji Mohammed Idris shi ne wanda zai jagoranci buɗe taron…
Read More

Zargin ɓatanci: Kotu ta ayyana 19 ga Yuni a matsayin ranar gurfanar da Natasha

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Babbar Kotun Tarayya a Abuja, ta ayyana 19 ga watan Yuni, 2025 a matsayin ranar da za a gurfanar da dakatacciyar Sanata, wato Natasha Akpoti-Uduaghan a gabanta. An maka ta ne a gaban kotun bisa tuhumar ta da laifin ɓata suna ga wasu sanannun jagororin siyasa. Gwamnatin Tarayya ta shigar da ita ƙara ne a kotun bisa zargin ta da furta kalaman ɓatanci akan shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio da kuma tsohon gwmanam jihar Kogi, Yahaya Bello. Da fari dai an zaɓi ranar 3 ga watan ne, inda daga bisani aka sauya lokacin saboda…
Read More

Emefiele ya samu sa’ida bayan Kotun Ɗaukaka Ƙara ta soke ƙwace wasu kadarorinsa

Emefiele ya samu sa'ida bayan Kotun Ɗaukaka ƙarar ta soke ƙwace wasu kadarorinsa Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Kotun Ɗaukaka Ƙara a Legas, ta soke umarnin ƙwace wasu kadarorin tsohon gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele da aka miƙa wa Gwamnatin Tarayya. A watan Nuwamban 2024 ne Babbar Kotun Tarayya a Legas ta yi hukuncin damƙa wa Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta'annati (EFCC) kadarorin Emefiele bisa zargin sa da mallakar su ba bisa doka ba. Jaridar NewsPoint Nigeria ta ruwaito kadarorin kamar haka; "The forfeited assets included two fully detached duplexes located at No. 17B,…
Read More