Tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Iran ta fara aiki, inji Trump

Spread the love

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Iran ta fara aiki.

Sai dai shugaban ya yi kira ga bangarorin biyu su mutunta yarjejeniyar

Donald Trump ya sanar da tsagaita buɗe wuta tsakanin Isra’ila da Iran a ranar Litinin da dare a shafinsa na sada zumunta.

Trump ya ce, Iran za ta fara aiwatar da tsagaita wutar, daga baya kuma Isra’ila za ta dakatar da kai wa Iran hari.

Isra’ila dai ta ci gaba da kai hare-hare cikin Iran, kamar yadda ministan tsaronta ya bayyana, yayin da kuma Iran ta yi gargaɗi ga mazauna birnin Ramat Gan kusa da Tel Aviv su fice, kamar yadda BBCHausa ta ruwaito.

By Babaji