Gwamnan Kano ya yi jimamin rasuwar ƴar jaridar BBC, Bilkisu Babangida

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya nuna kaɗuwarsa game da rashin ƴar jarida, marigayiya Hajiya Bilkisu Babangida, wadda ta rasu a yau, biyo bayan fama da rashin lafiya a Abuja.

Kakakin gwmnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya bayyana hakan a wata takarda, ranar Talata.

Gwamna Abba ya ce, marigayiyar mai shekaru 56, ta kasance ƙwararriyar ƴar jarida, wadda ta bar babban giɓi ga fannin aikin.

Ya kuma ce, tana amfani da aikinta wajen yaɗa labarai da haɗa kan al’umma gami da ɗaukaka muryoyinsu, yana mai cewa za a cigaba da tunawa da gudumawarta ga ɓangaren.

Haka kuma ya bayyana cewa, ayyukanta a VOA da BBC ya yi tasiri akan al’umma da dama, lamarin da ya yi sanadin ɗaukakarta a idon jama’a.

A madadin gwamnatin jihar da al’ummarta, gwamnan ya yi addu’ar Allah ya jiƙanta ya gafarta mata gami da bai wa iyalai, ƴan uwa da abokan arziƙi haƙurin juriyan rashin ta.

By Babaji