05
Jul
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya naɗa kyaftin ɗin Super Eagles, Ahmed Musa a matsayin sabon shugaban gudanarwar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars. A sanarwar da Kakakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya ce naɗin wani ɓangare ne nq ƙoƙarin ƙarfafa ƙungiyar gabanin fara sabuwar kakar Premier Nijeriya. Ya kuma ce, an naɗa Ahmed Musa ne, wanda ɗan wasan ƙungiyar ne, bayan tuntuɓar masu-ruwa-da-tsaki a harkokin wasanni a faɗin jihar. A watan Octoban 2024 ne Kano Pillars ta sanar da ɗaukar kyaftin ɗin na ƴan tawagar Nijeriya domin buga mata…
