06
Jul
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Dakatacciyar Sanatar Kogi, Natasha Akpoti-Uduaghan ta ci alwashin koma wa harkokin majalisa inda ta ce a ranar Talata za ta halarci zaman Majalisar Dattawa da aka saba yi. Natasha ta faɗi haka ne a wani gajeren faifan bidiyo da ta fitar, wanda ya karaɗe shafukan sada zumunta. A bidiyon, wanda aka gan ta tare da magoya bayanta, ta bayyana cewa, "Ina godiya da goyon bayanku. Ina farin ciki saboda mun yi nasara kasancewar kotu ta dawo da ni a yau." "Kuma za mu koma Majalisar Dattawa ranar Talata", inji ta. Duk da cewa ba…
