Babaji

5701 Posts

Tsohon gwamnan Oyo, Ladoja na shirin zama Olubadan na Ibadan bayan rasuwar Olakunlehin

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja A safiyar yau Litinin ne Oba Olakunlehin ya rasu, kwanaki biyu da cikar sa shekaru 90 a duniya. Lamarin da ya sa ake ganin tsohon gwamnan Jihar Oyo, Rashidi Ladoja ka iya zama wanda zai maye gurbinsa a matsayin sarki, wato Olubadan na Ibadan na gaba. A ranar 12 ga watan Yulin 2024 ne Gwamman Oyo, Injiniya Seyi Makinde ya naɗa Oba Olakunlehin a matsayin Olubadan na Masarautar Ibadan. Mutuwar Olakunlehin ta nuna cewa wanda zai gaje shi a kujerar yanzu shine Babban Alƙali, Rashidi Adewolu Ladoja, wanda ɗaya ne daga cikin manyan ƴan…
Read More

Asibitin Best Choice zai fara tiyata kala-kala da yin gagarumar rangwame ga marasa lafiya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Asibitin Best Choice zai fara yi wa marasa lafiya manyan tiyatu akan kuɗi kaso 50 bayan buɗe fayil kyauta da rage kuɗin ganin likita da wasu ayyukan da suka fara a satin da ya gabata. Yanzu haka asibitin ya sake tanadar kwararrun likitoci masu yin wadannan Tiyatar ( Urology) Aikin Mafitsara (Hynea) Qabar ciki (Orthopaedic) Aikin Qashi, (ENT) Aikin Hanci , Makogaro da Kunne (Dental) Hakori (Fibroid) Qarin mahaifa, (Urology) Aikin Mafitsara Asibitin ya zakulo zakakuran likitoci domin gudanar da wannan ayyukan daga yau Litinin 7, ga watan Yuli 2025, ga duk masu bukatar…
Read More

Ba mu yarda da karɓe iko daga haɗaka ƙarƙashin David Mark ba – Shugabannin ADC na jihohi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Rikici na neman ɓarkewa a jam'iyyar adawa ta ADC a yayin da shugabanninta na jihohi da dama suka nuna rashin amincewarsu game da sabunta tsarinta da sabuwar haɗaka ƙarƙashin jagorancin Atiku Abubakar ta yi. Jam'iyyar, wadda aka ƙarfafa da nufin fafatawa da Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027, ta fara fuskantar tsaiko daga jagorori a mataki na ƙasa. Hakan ya biyo bayan sanarwar da tsohon Shugaban jam'iyyar na Ƙasa, Ralph Nwosu ya yi na rushe tsare-tsaren jam'iyyar da nufin kafa ta ƙarƙashin ikon ƴan siyasar haɗaka da suka shiga cikinta a kwanan nan. Lamarin…
Read More

NNPCL ya rage farashin fetur a Abuja da wasu jihohi

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Babban Kamfanin Man Fetur na Ƙasa NNPCL, ya rage farashin litar fetur, inda ya ke sayerwa a Birnin Tarayya Abuja, Kaduna da Kano akan N910. Hakan na nufin an samu ragin Naira 35, wato ƙasa da N945 da ake sayerwa a baya. An ga yadda wasu gidajen mai suke sayerwa akan N935 a yankunan Lugbe da Airport Road dake birnin tarayyar. Lamarin da ya samu a sakamakon sauka da farashinsa ya yi a kasuwannin duniya, inda ganga guda na ɗanyen mai ya koma Dala 68.30 a ranar 4 ga watan Yuni. Akan haka ne…
Read More

NiMET ta yi hasashen ruwan sama da tsawa na kwana uku daga Litinin

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Hukumar kula da Yanayi ta Ƙasa (NiMET) ta ce ta yi hasashen samun mamakon ruwan sama haɗe da tsawa daga ranar Litinin zuwa Laraba a faɗin Nijeriya. A saƙon hasashen da ta fitar a Abuja, NiMET ta ce akwai yiwuwar samun hadari da tsawa a safiyar ranar Litinin a wasu yankunan Jihohin Taraba da Adamawa. Haka kuma, za a samu ruwan sama da tsawa a jihohin Zamfara, Adamawa, Kebbi, Taraba da Kaduna a yammacin Litinin. A shiyyar Arewa ta Tsakiya kuwa, ta yiwu a samu yayyafi da tsawa a wasu yankunan jihohin Abuja, Kogi,…
Read More

Haɗaka: Zulum ya musanta jita-jitar sauya sheƙa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya yi watsi da jita-jitar da ake yaɗawa a kafafen watsa labarai na cewa zai jagoranci wasu gwamnoni biyar zuwa jam'iyyar haɗakar ƴan adawa ta ADC. A sanarwar da Kakakinsa, Dauda Iliya ya fitar, Zulum ya bayyana raɗe-raɗin a matsayin ƙaryar da ba ta da asali ko tushe, wadda aka tsirar bisa wata manufa ta siyasa. Ya kuma jaddada cigaba da biyayya ga jam'iyya mai mulki ta APC a yayin gudanar da harkokin siyasarsa. Gwamnan, ya kirayi al'ummar jihar da na ƙasa baki ɗaya da su yi watsi…
Read More

NLC ta yi barazanar shiga yajin aiki bisa ƙamarin talauci da rashin tsaro

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa ta yi barazanar tsunduma cikin yajin aiki bisa tsadar rayuwa da rashin tsaro da suka addabi al'umma a Nijeriya. Ta yi gargaɗin cewa, ma'aikata ba za su cigaba da zura ido ba a yayin da harkar tattali da dimukraɗiyya suke tangal-tangal a ƙasar. NLC, kamar yadda ta bayyana a taron kwamitin ayyuka a Abeukuta, Jihar Ogun, ta ce halin matsin rayuwar da ma'aikata da talakawa suke fuskanta ya yi tsanani. Akan haka ne ta kirayi gwamnati da ta gaggauta ɗaukar matakan da suka dace wajen tabbatar da kawo ƙarshen hakan…
Read More

An kai jirgin Fadar Shugaban Ƙasa da ya shekara 20 Switzerland domin sayerwa

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta yi aike da jirgin sama na fadar gwamnati ƙirar 'Boeing 737-700 Business Jet (BBJ)' zuwa ƙasar Switzerland domin sayer da shi. Shahara Repoters ta ruwaito cewa, wani ƙwararre kan harkar cinikayyar jiragen sama ya sanya jirgin a matsayin ɗaya daga cikin waɗanda aka saka a kasuwa. Haka kuma, wani rahoto da jaridar IntelRegion ta fitar a yau Lahadi, ya bayyana cewa an sanya jirgin a sahun waɗanda za a sayer da su a shafin yanar gizo na wani ƙwararre akan harkar cinikayyar jiragen sama. Ƙwararren ya ce, a halin…
Read More

Taron BRICS: Tinubu ya ci alwashin magance matsalolin da ke daƙile bunƙasar noma da kiwo a Nijeriya

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Shugaba Bola Tinubu ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta cire baki ɗaya abubuwan da ke hana ci-gaba a fannin noma da bunƙasa harkar kiwo a Nijeriya domin bada damar shigowa da kayayyakin da suka shafi ɓangaren daga waje. A taron shugabannin ƙasashen BRICS da aka yi a Copacabana Forte a Brazil, wanda Shugaba Luiz Inacio Da Silva na ƙasar da wasu shugabanni suka halarta, Tinubu ya ce tsarin mataki-mataki, wato 'bureaucracy' yana taimaka wa samun jinkiri wajen cimma nasarori a fannin noma. Ya bayyana cewa, a halin yanzu yana ƙoƙarin samar da gyare-gyare…
Read More

Madrid za ta haɗu da PSG a wasan dab da na ƙarshe a Club World Cup

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid za ta haɗu da Paris Saint Germain a wasan dab da na ƙarshe biyo bayan nasarorin da suka yi a zangon dab da na kusa da na ƙarshe a ranar Asabar. Real Madrid ta yi nasara ne a lokacin da ake dab da kammala wasa tsakanin ta da Borussia Dortmund, inda aka tashi ci 3 da 2. PSG kuwa, ta yi nasarar doke Bayern Munich ne da ci 2 da 0 a wasan da suka yi a Atlanta. Madrid, wadda ta lashe kofin UEFA Champions League guda 15,…
Read More