14
Mar
Daga BELLO A. BABAJI Gwamnan Ribas, Siminalayi Fubara, ya sake aika saƙo ga Majalisar Dokokin jihar, inda ya ke sanar da ƴaƴanta batun ƙudirinsa na sake gabatar masu da kasafin 2025 don tantancewa da tabbatarwa. A saƙon, wanda ke ɗauke da ranar 13 ga watan Maris, gwamnan ya sanar da Kakakin Majalisar, Martin Amaewhule cewa ya zaɓi Laraba, 19 ga watan Maris, 2025 a matsayin ranar da zai sake gabatar da kasafin, wanda ya haifar da cecekuce a baya. Ya ce, ƴan majalisar za su iya zaɓar wata rana da ta fi dacewa da maslaharsu matuƙar wadda ya zaɓa ba…
