Babaji

5704 Posts

An sake zaɓar Motsepe a matsayin shugaban CAF

Daga BELLO A. BABAJI Shahararren Attajiri daga ƙasar Afirka ta Kudu, Patrice Motsepe ya sake zama Shugaban Hukumar Ƙwallon ƙafa ta Afirka (CAF), biyo bayan sake zaɓan sa da aka yi ba tare da abokin karawa ba. A shekarar 2021 ne aka zaɓe Motsepe mai shekaru 63 a matsayin shugaban CAF, inda ya sake jaddada aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar a watan Oktoban 2024. An tabbatar da shugabancin nasa ne a babban taron CAF da aka gudanar a birnin Cairo a ƙasar Misira, wanda ya samu halartar shugaban Hukumar Ƙwallon ƙafa ta Ƙasa-da-ƙasa (FIFA), Gianni Infantino, ranar Laraba. Baya ga…
Read More

‘Yan sanda sun kashe ƙasurgumin mai garkuwa da mutane a Abuja, Dogo Saleh

Daga BELLO A. BABAJI Ƴan sanda a Abuja, sun samu gagarumar nasara a ƙoƙarinsu na daƙile ayyukan ta'addanci a babban birnin, inda suka kashe shahararren mai garkuwa da mutane, Dogo Saleh. Kakakin rundunar, SP Josephine Adeh ta faɗi hakan a wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba, inda ta tabbatar wa mazauna yankin cewa jami'ansu na aiki tuƙuru wajen magance ƴan ta'adda da ayyukansu a birnin da ma maƙota jihohi. Ta ce, sun kashe ɗan bindigar ne bayan samun wani rahoton sirri, sakamakon ayyukansa na ta'addanci da garkuwa da mutane a babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna, Lokoja da Enugu…
Read More

‘Yan majalisa a Ribas sun rufe ƙofa don kada Gwamna Fubara ya shiga zauren majalisarsu

Daga BELLO A. BABAJI A ranar Laraba ne wani abu mai kama da wasan kwaikwayo ya faru Ribas, inda Gwamna Siminalayi Fubara ya je zauren Majalisar Dokokin jihar inda ya tarar da ƙofar shiga a kulle. Rahotanni sun bayyana cewa, jami'an tsaro ne suka kulle ƙofar a lokacin da tawagar gwamnan ta isa zauren. Jami'an sun ce sun yi hakan ne saboda ba a samu wani saƙo ko tattaunawa ta musamman a tsakanin gwmnan da majalisar ba. Saidai, Gwamna Fubara ya ce ya aika saƙo zuwansa ga Kakaki Martins Amaewhule da kuma ƙoƙarin kiran sa ta waya tun a ranar…
Read More

Nijeriya ta hau sabon tsanin cigaba, inji Shettima

Daga BELLO A. BABAJI Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shatima ya bayyana hakan a yayin da ya karɓi baƙoncin takwaransa Mataimakin Shugaban ƙasar Brazil, Geraldo Alckmin don tattaunawa kan yadda za a sabonta dabarun cin gajiyar dangantaka tsakanin Nijeriya da Brazil. Tawagar ta Brazil ta haɗa manyan jagorori a ɓangarorin gwamnati da masu zaman kansu na ƙasar. Baƙin sun biyo sawu ne sakamakon tsaikon da aka samu a ɓangaren zartar da yarjejeniyoyin da aka cimma na tsawon shekaru. A jawabinsa, Kashim Shatima ya bayyna cewa, Shugaba Bola Tinubu mutum ne wanda ya nuna ƙwarewa da jajircewa wajen samar wa ƴan Nijeriya…
Read More

Gwamatin Tarayya ta shirya kammala aikin madatsar ruwa ta Dasin Hausa a Adamawa

Daga BELLO A. BABAJI Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta shirya kammala aikin madatsar ruwa ta Dasin Hausa dake jihar Adamawa. Aikin, wanda aka dakatar tun a shekarun 1980s, zai magance matsalolin ambaliyar ruwan da ke fitowa daga madatsar ruwa ta Lagdo a Kamaru. Rahotanni sun bayyana cewa, Ma'aikatar Albarkatun Ruwa da Hukumar ICRC da gwamati za su haɗa gwiwa da kamfanin Mainstream Energy don kammala aikin a kan lokaci, a ƙarƙashin tsarin haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu (PPP). Kmmala Madatsar ruwan, zai taimaka wajen samar da wutar lantarki mai ƙarfin megawatt 300, kana ta bayar da…
Read More

Sojoji sun kashe gomman ƴan bindiga da tarwatsa maɓoyarsu a Zamfara

Daga BELLO A. BABAJI Dakarun haɗaka na Atisayen 'FANSAN YAMMA' a Zamfara, sun samu nasarar hallaka ƴan bindiga da dama a maɓoyarsu dake gabashin Ƙaramar Hukumar Ƙauran-Namoda a jihar. A ranar 10 ga watan Maris ne jami'an suka kai harin, wanda ya yi sanadin mutuwar ƴan ta'addar da ƙwato makamai da wasu ababe. Dakarun, waɗanda ke aiki a ƙarƙarshin Birget ta 1, sun kai farmakin ne ta sama da ta ƙasa a maɓoyar babban ɗan ta'adda, Ɗan Sa'adia. Daga cikin waɗanda aka kashe a yayin farmakin akwai shahararren ɗan bindiga mai suna Babangida. Harin dakarun ya sa an ƙwato ƙaramar…
Read More

Sai mun saurari ɓangaren Akpabio kafin mu ɗauki mataki na gaba – Majalisar dokoki ta duniya

Daga BELLO A. BABAJI Majalisar Dokoki ta Majalisar Ɗinkin Duniya (IPU), ta ce za ta yi aiki akan ƙorafin da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta shigar a wajenta kan dakatarwar da Majalisar Dattawan Nijeriya ta yi mata na wata shida da zargin cin zarafi da ta yi akan Shugaban majalisar, Godswill Akpabio. A lokacin da ta ke magana a taron mata na IPU da aka yi a Birnin New York na Amurka, Natasha ta sanar da IPU batutuwan biyu da suka samo asali daga tsarin zama a zauren Majalisar Dattawan, inda ta bayyana dakatarwar a matsayin abinda aka mata ba bisa…
Read More

Natasha ta miƙa batun rikicinta da Akpabio ga majalisar dokoki ta duniya

Daga BELLO A. BABAJI Sanatar da aka dakatar daga Majalisar Dattawan Nijeriya, Natasha Akpoti-Uduaghan, wadda ke wakiltar Jihar Kogi ta Tsakiya, ta kai batun rikicinta da Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio zuwa mataki na duniya. Ta yi hakan ne a yayin zaman majalisar dokoki ta Majalisar Ɗinkin Duniya da ke bai wa mata daman gabatar da batutuwansu, wanda aka gudanar a birnin New York. Ta ce, tana neman a yi mata adalci ta hanyar shigo da cibiyoyin demokraɗiyya a mataki na duniya cikin batun. Ta kuma bayyana dakatar da ita daga Majalisar Dattawan a matsayin abinda aka yi ba bisa doka…
Read More

Kocin Super Eagles ya ajiye Ahmad Musa, ya zuba ƴan wasan gida a jerin ƙarshe na wasannin neman gurbi a Kofin Duniya

Daga BELLO A. BABAJI Kocin Super Eagles, Éric Sekou Chelle, ya soke sunan Kyaftin ɗin tawagar, wato Ahmad Musa a matsayin ɗaya daga cikin waɗanda za su fafata a wasannin neman gurbin shiga gasar Kofin Duniya na 2026. Super Eagles za ta buga wasanni biyu ne da ƙasashen Ruwanda da Zimbabwe a watan Maris. A ranar 21 ga wata ne ƙungiyar za ta fafata da takwararta ta ƙasar Ruwanda, bayan kwanaki huɗu kuma za ta buga da Zimbabwe a Filin wasa na Godswill Akpabio dake Uyo a Jihar Akwa-Ibom. Ga tawagar ƴan wasa 23 da kocin ya zaɓo a jerin…
Read More

Kwankwaso ne ɗan takarar da ya fi cancanta a maja, inji tsohon shugaban ANP

Daga BELLO A. BABAJI Tsohon Shugaban tsohuwar jam'iyyar ANP na ƙasa, kuma Darakta-Janar na yaƙin neman zaɓen Rabi'u Musa Kwankwaso a NNPP a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, Asiwaju Moshood Shittu, ya roƙi jam'iyyun adawa da ke shirin dunƙulewa don kayar da Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027 da su zaɓi Kwankwaso a matsayin ɗan takara matuƙar suna neman nasara. Moshood ya yi kiran ne a yayin taron manema labarai, inda ya ce Kwankwaso ne kaɗai wanda ya ke da nagartar da zai iya tunkarar Tinubu a zaɓen 2027 la'akari da gogewarsa a ɓangarori da dama na harkar siyasa da…
Read More