11
Mar
Daga BELLO A. BABAJI Tsohon Shugaban tsohuwar jam'iyyar ANP na ƙasa, kuma Darakta-Janar na yaƙin neman zaɓen Rabi'u Musa Kwankwaso a NNPP a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, Asiwaju Moshood Shittu, ya roƙi jam'iyyun adawa da ke shirin dunƙulewa don kayar da Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027 da su zaɓi Kwankwaso a matsayin ɗan takara matuƙar suna neman nasara. Moshood ya yi kiran ne a yayin taron manema labarai, inda ya ce Kwankwaso ne kaɗai wanda ya ke da nagartar da zai iya tunkarar Tinubu a zaɓen 2027 la'akari da gogewarsa a ɓangarori da dama na harkar siyasa da…
