10
Mar
Daga BELLO A. BABAJI Iyalan marigayi tsohon shugaban mulkin soji, Janar Sani Abacha, sun mayar da martani kan kalaman Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) na cewa Abacha ne ke da alhakin soke zaɓen Shugaban ƙasa na ranar 12 ga watan Yulin 1993. A littafinsa da ya fitar a kwanan nan mai suna 'A journey in Service', IBB ya yi da-na-sanin soke zaɓen, tare da tabbatar da ɗan takarar jam'iyyar SDP, wato MKO Abiola a matsayin wanda ya lashe zaɓen. A lokacin da ya ke bayyana yadda tarihin lamarin ya kasance, IBB ya ɗora wa sojoji a ƙarƙashin jagorancin Abacha laifi,…
