Babaji

5706 Posts

Wani mutum ya kashe ‘admin’ saboda cire shi a guruf ɗin WhatsApp

Daga BELLO A. BABAJI A ranar Asabar ne ƴan sanda a Nahiyar Asiya suka sanar da cewa ce, an kama wani ɗan Pakistan bisa zargin sa da laifin kisa ta hanyar harbe wani admin ɗin dandalin Whatsapp. An harbe Mushtaq Ahmed ne a maryacen ranar Alhamis a garin Peshawar na birnin Khyber Pakhtunkwa dake kan iyaka da ƙasar Afghanistan, wanda ke da tarihi na zubar da jini a tsakanin al'umma. Ana dai tuhumar wani mai suna Ashfaq ne da kisan mamacin, kamar yadda rahoton ƴan sandan ya nuna. Wani ɗan'uwa ga Mushtaq ya ce, an kashe mamacin ne biyo bayan…
Read More

Shugaba Tinubu ya yi alhinin rasuwar Sheikh Sa’idu Jingir

Daga BELLO A. BABAJI Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya jajenta wa al’ummar musulmi bisa rasuwar shahararren Malamin addinin musulunci kuma Mataimakin Shugaban Majalisar Malamai ta ƙungiyar JIBWIS reshen Jos, Sheikh Sa’idu Hassan Jingir, wanda ya rasu ranar Alhamis. Wata sanarwa da ta fito daga fadar Shugaban da ke ɗauke da sanya hannun mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ta bayyana Sheikh Jingir a matsayin shugaban addini mai himma wajen karantarwa da yaɗa koyarwar addinin Musulunci da kyawawan ɗabi'u ga mabiya. Shugaban ya ƙara da cewa, "Sheikh Jingir shugaba ne mai mai tawali'u da sadaukar da…
Read More

Sojoji sun kashe jagoran Lakurawa

Daga BELLO A. BABAJI Gamayyar Jami'an tsaro sun yi nasarar kashe jagoran ‘yan bindiga na Lakurawa, wato Mai-Gemu, a jihar Kebbi. Daraktan Tsaro na Ofishin Majalisar Zartarwa, AbdulRahman Usman-Zagga, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, a Birnin Kebbi. Ya ce, an kashe Mai-Gemu ne a ranar Alhamis a yankin Kuncin-Baba dake Karamar Hukumar Arewa, bayan artabu mai tsanani da jami’an tsaro. Ƙungiyar Lakurawa dai wata ƙungiyar ‘yan ta’adda ce da ta shigo Sokoto da Kebbi ta mashigar Jamhuriyar Nijar, lamarin da ke ƙara ta’azzara matsalar rashin tsaro a yankin Arewa maso Yammacin Nijeriya.…
Read More

‘Yan hidimar ƙasa za su yi aikin ƙidaya, yayin da Tinubu ya ƙi amincewa da kasafin NPC

Daga BELLO A. BABAJI Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ƙi amincewa da kasafin Naira biliyan 942 da Hukumar Ƙidaya ta Ƙasa (NPC) ta gabatar domin gudanar da ƙidayar gidaje da mutane a ƙasar. Hakan ya biyo bayan tattauanawa da manyan jami'an NPC da Tinubu ya yi a ranar 24 ga watan Fabrairu a Fadar Shugaban ƙasa, inda ya nace akan sai dai a nami hanyar rage adadin kuɗin. Wasu muryoyi sun bayyana cewa, Shugaba Tinubu ya nemi da sanya ƴan hidimar ƙasa (ƴan NYSC) a matsayin waɗanda zasu gudanar da aikin ƙidayar, wanda akwai yiwuwar hakan ya tabbata kuma ya…
Read More

Tinubu ya naɗa Jega a matsayin mai taimaka masa kan harkokin kiwo

Daga BELLO A. BABAJI Shugaba Bola Tinubu ya naɗa tsohon shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Attahiru Jega a matsayin Mai taimaka masa kuma Kodineta kan harkokin Kiwo. Mai taimaka wa Shugaban kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga ya wallafa hakan ta kafar X, ranar Juma'a. Daga shekarar 2010 zuwa 2015 ne Jega ya riƙe muƙamin shugaban INEC. Haka kuma a watan Yulin 2024 ne Shugaba Tinubu ya samar da sabuwar ma'aikata mai suna Ma'aikatar Ci-gaban Kiwo. An samar da ita ne musamman don warware matsalolin da suka jima suna faruwa a tsakanin makiyaya da manoma a sassan Nijeriya.
Read More

Tsagaita wutar yaƙin Ukraniya: Trump ya yi wa Rasha barazana da ƙarin farashi

Daga BELLO A. BABAJI Shugaba Donald Trump na Amurka ya yi wa ƙasar Rasha barazanar sanya mata takunkumi na yin wasu hukunce-hukunce da ƙara farashi a ɓangarori matuƙar ta ƙi amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta a yaƙinta da Ukraniya. A wani rubutu da aka wallafa a 'Truth Social', ranar Juma'a, Trump ya yi wa ƙasashe biyun kiranye da su gaggauta shirya tattaunawa kan dakatar da yaƙin a tsakanin su. Ya ce, la'akari da yadda ake ƙwarar Ukraniya yayin da ake fafatawa, zai samar da wasu hukunce-hukunce na banki da na wasu ɓangarori da hawar da farashin abubuwa ga Rasha har…
Read More

A karo na biyu cikin 2025, rumbun lantarki na ƙasa ya lalace

Daga BELLO A. BABAJI A ranar Juma'a ne ƴan Nijeriya suka sake samun kansu a yanayi na duhu sakamakon tsaiko da rumbun wutar lantarki na ƙasa ya samu a wani wuri karo cikin 2025. Manyan kamfanonin raba lantarki na Ikeja da Eko sun tabbatar da aukuwar lamarin, wanda ya faru da misalin ƙarfe 4 na yamma. A sanarwar da Kamfanin raba Wutar lantarki na Ikeja ya yi ta shafin X, ya shaida wa kwastomominsa cewa, sun samu tsaiko ne tun daga ƙarfe 2 na rana, amma jami'ansu da haɗin-gwiwar masu-ruwa-da-tsaki na aikin gyarawa. Haka ma na Eko, wanda ya ce…
Read More

Eto’o ya yi nasara a kotu da zama halasttaccen ɗan takara a zaɓen CAF

Daga BELLO A. BABAJI A ranar Juma'a ne Kotun Alƙalanci ta Wasanni ta umarci Hukumar Ƙwallon ƙafa ta Afirka (CAF), da ta ƙyale Shugaban Hukumar Ƙwallon ƙafa ta Kamaru, Samuel Eto'o ya zama ɗan takara a majalisarta ta zartaswa. CAF ta ƙi amincewa da tsayawa takara da tsohon gwarzon ɗan wasa na Afirka ke ƙoƙarin yi, kasancewar shi ne shugaban hukumar ƙwallon ƙasarsa tun a shekarar 2021. A mako na gaba ne CAF za ta gudanar da zaɓe a babban zaman da ta shirya. Eto'o mai shekaru 43, wanda kuma tsohon ɗan wasan ƙungiyar Barcelona ne, na hali na rikici…
Read More

PDP ta yi tir da dakatar da Sanata Natasha, ta zargi Akpabio da rufa-rufa

Daga BELLO A. BABAJI Babbar Jam'iyyar adawa, wato PDP, ta yi alla-wadai da dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan daga Majalisar Dattawa sakamakon zargin cin zarafi da ta yi akan Shugaban majalisar, Godswill Akpabio. A ranar Alhamis ne majalisar ta sanar da dakatar da Sanata Natasha na tsawon watanni shida bayan samun ta da laifin taka wasu daga cikin dokokinta. Hakan ya biyo bayan rikicinta ne da Akpabio, wanda ta zarga da yunƙurin cin zarafin ta duk da cewa daga bisani ya musanta batun. A sanarwar da Sakataren yaɗa labaran PDP na ƙasa, Debo Ologunagba ya fitar a ranar Juma'a, jami'yyar…
Read More

Fashewar tankar mai ya sake sanadin mutuwar mutum bakwai a Neja

Daga BELLO A. BABAJI A yammacin ranar Alhamis ne wata tankar man fetur ta tarwatse a ƙauyen Ƙaramin Rami na ƙaramar hukumar Mashegu a jihar Neja, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane bakwai. A wata takarda da Darakta-Janar na Hukumar bada Agajin Gaggawa ta jihar, Abdullahi Baba Arah ya fitar, ya ce lamarin ya auku ne a lokacin da tankar ta yi ƙoƙarin canza hannu sakamakon rashin kyan hanya, inda ta faɗi tare da kwararar da man da ke cikin ta a wani wajen da manoman rani na shinkafa ke aiki. Ya ce, man da ke zubar ya haɗe…
Read More