
Daga BELLO A. BABAJI
Gamayyar Jami’an tsaro sun yi nasarar kashe jagoran ‘yan bindiga na Lakurawa, wato Mai-Gemu, a jihar Kebbi.
Daraktan Tsaro na Ofishin Majalisar Zartarwa, AbdulRahman Usman-Zagga, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, a Birnin Kebbi.
Ya ce, an kashe Mai-Gemu ne a ranar Alhamis a yankin Kuncin-Baba dake Karamar Hukumar Arewa, bayan artabu mai tsanani da jami’an tsaro.
Ƙungiyar Lakurawa dai wata ƙungiyar ‘yan ta’adda ce da ta shigo Sokoto da Kebbi ta mashigar Jamhuriyar Nijar, lamarin da ke ƙara ta’azzara matsalar rashin tsaro a yankin Arewa maso Yammacin Nijeriya.
A baya, bayanan Sojojin sun yi nuni da cewa, ana samun nasarori a yaƙin da suke da tsagerun ƙungiyar.