
Daga BELLO A. BABAJI
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya jajenta wa al’ummar musulmi bisa rasuwar shahararren Malamin addinin musulunci kuma Mataimakin Shugaban Majalisar Malamai ta ƙungiyar JIBWIS reshen Jos, Sheikh Sa’idu Hassan Jingir, wanda ya rasu ranar Alhamis.
Wata sanarwa da ta fito daga fadar Shugaban da ke ɗauke da sanya hannun mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ta bayyana Sheikh Jingir a matsayin shugaban addini mai himma wajen karantarwa da yaɗa koyarwar addinin Musulunci da kyawawan ɗabi’u ga mabiya.
Shugaban ya ƙara da cewa, “Sheikh Jingir shugaba ne mai mai tawali’u da sadaukar da kai da tsantseni, wanda ya samo halayen nasa daga ilimin addinin Islama.”
“Hakika Addinin Musulunci ya yi rashin wani turke mai girma, kuma babban jagora da babu abinda zamu bi shi da shi sai addu’ar Allah Ya jiƙansa, kuma kyawawan ayyukansa su bi shi,” inji Shugaba Tinubu.
