Babaji

5706 Posts

Majalisar Wakilai na shirin karɓe ikon gudanarwa da rajistar jam’iyyu a hannun INEC

Daga BELLO A. BABAJI Majalisar Wakilai ta fara shirin karɓe iko daga Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) na gudanarwa da yin rajista ga jam'iyyun siyasa a Nijeriya. A ranar Alhamis ne ƙudirin da ke neman samar da hukuma ta musamman kan alhakin kula da gudanarwar jam'iyyu da ɗaukar nauyinsu ya tsallake karatu na biyu a majalisar. Ƙudirin, wanda Kakakin majalisar, Tajuddeen Abbas da ɗan majalisa Markus Onobun daga Jihar Edo suka ɗauki nauyinsa, na neman a daina yin rajistar jam'iyyu da kula da su daga hannun INEC. Haka kuma, ya na neman a samar da kwamitin shari'a na warware matsalolin…
Read More

‘Yan Nijeriya ne suka fi shan tsadar tikitin jirgi a Afirka, inji NCAA

Daga BELLO A. BABAJI Hukumar Kula da Zirga-zirgar Jiragen sama ta Ƙasa, NCAA, ta yi ƙorafi game da yadda wasu kamfanonin jiragen sama suke ƙin kula da fasinjoji ƴan Nijeriya tare da cewa sune suke biyan kuɗi mafi tsada a Afrika. Daraktan yaɗa labarai na NCAA, Michael Achimugu ya bayyana hakan a yayin ganawa da hukumar gudanarwar Kamfanin RwandAir wanda ya ɗauki tsawon lokaci na mayar wa wasu fasinjojin Nijeriya kuɗaɗensu. Ya koka gami da nuna rashin ƙwarewa da jami'an kamfanin suka nuna, wanda shi ya sabbaba jinkirin biyan fasinjojin kuɗaɗensu. Rahotonni sun bayyana cewa kamfanin RwandAir na fama da…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Tsohon mataimaki ga Obasanjo, Okupe ya rasu

Daga BELLO A. BABAJI Tsohon mai taimaka wa tsohon Shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, Dakta Doyin Okupe ya rasu. A safiyar ranar Juma'a ne Dakta Okupe, mai shekaru 72 ya rasu, bayan fama da wani gajeren rashin lafiya da ake kyautata zaton cutar daji ce. A shekarar 2022 ne aka naɗa shi a matsayin Darakta-Janar na jam'iyyar LP na zaɓen Shugaban ƙasa na 2023. Daga bisani aka tilasta masa yin murabus sakamakon zarginsa da badaƙalar wasu kuɗaɗe.
Read More

Rahoton MƊD ya bayyana munanan hare-hare akan Musulmi da ƴan gudun hijira

Daga BELLO A. BABAJI Wani rahoto da Majalisar Ɗinkin Duniya (MƊD) ta fitar a ranar Laraba, ya tono yadda aka samu cin zarafin ƴan ɗan-adam daga ƙungiyoyin ƴan ta'adda a yankin Kudu maso Gabas na Jamhuriya Afirka ta Tsakiya, waɗanda musamman hare-hare ne da suka fi shafar inda al'ummar Musulmi suke da kuma ƴan gudun hijira na ƙasar Sudan. Binciken da ofishin ƴancin ɗan-adam na MƊD (OHCHR) ya da na jami'an wanzar da zaman lafiya a ƙasar, MINUSCA, ya bayyana hujjoji na kashe-kashe da cin zarafin ƴan'uwa mata da kuma duka. Sauran sun haɗa da tsangwamar su da tilasta masu…
Read More

Majalisa abar girmamawa ce – Matar Shugaban ƙasa ga Natasha

Daga BELLO A. BABAJI Matar Shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta ce Majalisar Dattawa ta na ɗaukar matakan da suka dace game da zargin cin zarafi da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi akan Shugaban majalisar, Godswill Akpabio. A lokacin da ta ke tsokaci kan batun a Abuja, ranar Alhamis, Sanata Remi ta ce, Majalisar Dattawa a matsayinta na babbar zauren dokoki a Nijeriya, waje ne da bai kamata a ce irin haka ya faru ba. Ta ce, lallai ta na sane da abinda ke faruwa a majalisar kuma jagororinta suna ɗaukar matakan da suka dace akan al'amarin. Ta kuma ce,…
Read More

Tinubu ya amince da tallafin kaso 80 ga masu jinyar cutar ƙoda

Daga BELLO A. BABAJI Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da samar da tallafi ga ƴan Nijeriya da ke yin jinyar cutar ƙoda, waɗanda daga yanzu za su riƙa biyan N12,000 a madadin N50,000. Tuni aka fara aiwatar da shirin hakan a wasu cibiyoyin kiwon lafiya a shiyyoyi shida na Nijeriya. Jaridar 'Intelregion' ta ruwaito cibiyoyi da asibitocin da suka fara aiwatarwa kamar haka;"…Federal Medical Centre (FMC) Ebute-Metta Lagos, the Federal Medical Centre (FMC) Jabi, Abuja, the University College Hospital (UCH) Ibadan, the Federal Medical Centre (FMC) Owerri, and the University of Maiduguri Teaching Hospital (UMTH) Maiduguri." Sauran sun haɗa…
Read More

Majalisar Dattawa ta dakatar da Sanata Natasha na wata shida

Daga BELLO A. BABAJI Majalisar Dattawa ta dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan na tsawon watanni shida kan rikicinta da Shugaban majalisar, Godswill Akpabio. Akpabio ya bayyana hakan a lokacin hukunci kan sakamakon binciken kwamitin ladabtarwa, wanda ya nuna cewa Natasha ta saɓa wa dokokin tsayawa na 2023 na majalisar. Duk da cewa, wasu daga cikin sanatoci sun yi ƙoƙarin ganin an rage adadin lokacin dakatarwar zuwa watanni uku, amma hakan bai samu ba saboda mafiya rinjaye sun tafi akan hukuncin farko. Ana ganin cewa akwai yiwuwar a rage adadin lokacin ko kuma a soke dakatarwar baki ɗaya matuƙar Natasha ta…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Majalisar Dattawa na yunƙurin dakatar da Sanata Natasha

Daga BELLO A. BABAJI Majalisar Dattawa na duba yiwuwar dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan na tsawon watanni shida. Hakan ya biyo bayan bincike ne da kwamitin ladabtarwa na majalisar ya gudanar a kanta, wanda ya ce an same ta da karya wasu daga cikin dokokin majalisar. Shugaban kwamitin, Neda Imasuen, ya ce za a rufe ofishinta da kuma haramta mata zuwa farfajiyar majalisar a yayin dakatarwar. Sannan, za a daina biyan ta kuɗaɗen albashi da na mataimakanta zuwa lokacin da wa'adin zai ƙare. Kazalika, za a hana ta wakiltar Nijeriya a kowane aiki a matsayinta na sanata, duk a cikin…
Read More

Gwamnan Katsina ya jaddada aniyar gwamnatinsa ta ƙin yin sulhu da ƴan ta’adda

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamna Dikko Raɗɗa ya sake nanata matsayin gwamnatinsa na ƙin sasantawa da ƴan ta'adda da suka lalata wasu sassan jihar. Ya faɗi haka ne a garin Jibiya a lokacin ƙaddamar da bada tallafin kayan abinci da Ɗan Majalisar Dokoki na jihar, Hon. Mustapha Yusuf ya samar wa al'ummar mazaɓarsa. Ya ce, gwamnati ba za ta sasanta da yan ta'adda ba, amma ƙofa a buɗe take kan duk wanda yake son ya ajiye makamansa. "Gwamnati na maraba ga duk ɗan ta'addan da ke son aje makaminsa domin shiga cikin al'umma ya cigaba da rayuwarsa kamar yadda…
Read More

Dujiman Katsina ya samar wa matasa aiki a hukumomin tsaro na ƙasa

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Shugaban kwamitin harkokin cikin gida na Majalisar Wakilai kuma Dujiman Katsina, Hon. Abdullahi Aliyu ya samar wa matasa 175 aiki a hukumomin tsaro. Hukumomin sun haɗa da hukumar kashe Gobara ta ƙasa, ƴan Sanda, Sojoji, Asibitin gwamnatin tarayya da Asibitin Koyarwa na Gwamnatin Tarayya. Ɗan majalisar, wanda shi ke wakiltar Musawa da Matazu ya ce, mutane 42 sun samu aiki a hukumar kashe gobara ta ƙasa, sai wasu 18 a hukumar shige da fice, sai kuma mutane 100 a Soja da sauran ma'aikatun Gwamnatin Tarayya. A wata takarda da ke ɗauke da sa hannun mataimakinsa…
Read More