Babaji

5706 Posts

Lantarkin Nijeriya ya kai megawat 6003 – Gwamnatin Tarayya

Daga BELLO A. BABAJI Gwamnatin Tarayya ta ce ta samu raba adadin wutar lantarki mafi girma a tarihin Nijeriya, wanda ya kai megawat 6,003. Ministan Wutar lantarki, Cif Adebayo Adelabu ya bayyana hakan a wata takarda da Mai taimaka masa akan Sadarwa, Bolaji Tunji ya fitar, inda ya ce hakan wata gagarumar nasara ce a lokacin da Nijeriya ta samu adadin megawat 5,801.84 wanda ke ba ta damar raba lantarki na megawat 128,370.75 a kullum. Ya ce, waɗanda nasarori suna wakiltar bunƙasa da ɓangaren ya samu don biyan buƙatu na wuta ga al'ummar ƙasa da kuma ƙoƙarin gwamnatin Shugaba Bola…
Read More

Iyalan ɗan TikTok ɗin da ya yi ɓatanci sun nemi yafiyar Kannywood

Daga BELLO A. BABAJI Iyalan ɗan TikTok, Ahmed Ataye Na-Madina, wanda ake kira da Titanic, sun barranta kawunansu daga kalaman ɓatancin da ya fitar ta kafar soshiyal mediya. A halin yanzu, Na-Madina yana tsare a hannun hukuma, a Jos, Babban Birnin Jihar Filato. A wani faifan bidiyo, an ga inda mahaifinsa wanda ba a bayyana sunansa ba, yana cewa, suna neman masana'antar Kannywood da ta yafe wa ɗan nasu kuma suna alla-wadai da abinda ya aikata. Ya roƙi jagorori da mambobin masana'antar da su yi haƙuri su yafe masa albarkacin watan Ramadan da al'umma suke gudanar da azumi a cikinsa.
Read More

Majalisar Dattawa ta yi watsi da ƙorafin Natasha akan Akpabio

Daga BELLO A. BABAJI Kwamitin Kula da Ƙwarewa da bin dokoki da sauraron ƙorafi na Majalisar Dattawa, ya yi watsi da ƙorafin da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta shigar na cin zarafi da rashin mutunta aiki akan Shugaban majalisar, Godswill Akpabio. A ranar Laraba ne kwamitin ya bayyana cewa, akwai saɓa wa aiki acikin al'amarin, inda Shugabansa, Neda Imasuen ya ce Natasha ce wadda ta sanya hannu akan takardar ƙorafin a madadin bai wa wani daban, kamar yadda dokar majalisar ta ayyana. Haka kuma ya ce, maganganun da ta yi a takardar ƙorafin, tuni aka miƙa su kotu gabannin a gabatar…
Read More

Rashin samar da wadatattun kayan shan ruwa ya tunzura kwamashina a Jigawa

Daga UMAR AƘILU MAJERI a Dutse Kwamashinan ayyuka na musamman, Alh Auwalu Danladi Sankara ya nuna damuwarsa kan yadda ake yi wa gwamnatin jihar zagon kasa ta fuskar ciyar da al'umma abinci a lokacin buɗe baki a mazabun da gwamnatin ta ware guda 634 albarkacin wata Ramadan. Kamar yadda ya wallafa shafinsa na Facebook, Sankara ya ce "Mun samu labari da rahotanni na wasu cibiyoyi da ke samar da abincin shan ruwa (buɗa baki) da ba su cika ba a lokacin shirin ciyarwa na watan Ramadan da gwamnatin Jihar Jigawa ta shirya. A ƙasa akwai cibiyoyin da dillalan da suke…
Read More

A karon farko, Akpabio ya magantu kan zargin cin zarafin Natasha

Daga BELLO A. BABAJI Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya musanta batun zargin cin zarafi da Sanatar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi akansa. Akpabio ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, a yayin zaman majalisar bayan hutun mako guda, inda ya ce bai taɓa cin zarafin kowacce mace ba. Ya ce, shi mutum ne da mace ta raina, don haka yana matuƙar girmama mata, kuma hakan ya sa aka taɓa ba shi kyautar gwamnan da ya fi kowane gwamna iya kula da buƙatun jinsi a Nijeriya. Ya shelanta cewa, bai taɓa yunƙurin aikata alfasha da Sanata Natasha ko…
Read More

Natasha: Kotu ta umarci kwamitin bincike ya dakata

Daga BELLO A. BABAJI Babbar Kotun Tarayya dake Abuja ta umarci kwamitin bincike akan ƙwarewar aiki na Majalisar Dattawa da ya dakata da shirinsa na gudanar da bincike akan kalaman Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan. Alƙali Obiora Egwuatu ya bada umarnin a wata takarda a ranar Talata a matsayin amsa ga ƙarar da lauyoyin Natasha, wadda ke wakiltar Kogi ta Tsakiya suka shigar. Hakan na zuwa ne a lokacin da kwamitin ya shirya dakatar da Sanatar na wani lokaci, wanda hakan ya sa za a dakatar da kowane aiki akan batun har zuwa sadda shari'a za ta bada damar cigaba. A baya…
Read More

Majalisar Dattawa ta ce ba za ta binciki Akpabio kan zargin cin zarafin Natasha ba

Daga BELLO A. BABAJI Majalisar Dattawa ta ce ba za ta gudanar da bincike akan Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio ba, wanda aka zarge shi da cin zarafin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, saboda ba a shigar mata da ƙara a rubuce ba. Shugaban kwamitin yaɗa labarai na majalisar, Sanata Yemi Adaramodu (APC, Ekiti ta Kudu) ya bayyana hakan a yayin hira da gidan talabijin na Arise a ranar Litinin, inda ya ce wajibi ne kowane ɗaya daga cikin mambobin majalisar ya kula da irin kalaman da za su riƙa fitowa daga bakinsa. Ya ce, a matsayinsu na cibiya, ba za su tanka…
Read More

Ahmed Musa ya shiga sahun ƴan Super Eagles da za su fafata a wasannin neman gurbin shiga gasar Kofin Duniya

Daga BELLO A. BABAJI Kocin Super Eagles, Éric Sékou Chelle ya zaɓi masu tsaron gida Stanley Nwabali da Adeleye Adebayo, da ƴan wasan baya William Ekong, Calvin Bassey da kuma Olaoluwa Aina Sai ƴan wasan tsakiya Alex Iwobi da Wilfred Ndidi, da kuma na ƴan wasan gaba Ademola Lookman, Victor Osimhen and Simon Moses daga cikin jaddawalin ƴan wasa 39 da za su buga wasannin neman gurbin shiga gasar Kofin Duniya na 2026 da ƙasashen Rwanda and Zimbabwe da za a yi a wannan watan. Haka kuma, akwai gola Maduka Okoye da ƴan baya da suka haɗa da Bruno Onyemaechi…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Shugaba Tinubu ya naɗa sabon akanta-janar na ƙasa

Daga BELLO A. BABAJI Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Shamseldeen Babatunde Ogunjimi a matsayin sabon Akanta-janar na Ƙasa (AGF) biyo bayan tantancewa mai fadi da aka gudanar akansa. Naɗin Ogunjimi, wanda aka tabbatar a ranar 4 ga watan Maris, zai fara aiki ne a ranar 7 ga watan Maris, 2025, kuma a ranar ne mai barin gado, Oluwatoyin Madehin zai yi ritaya. A watan Disambar da ta gabata ne aka ayyana Ogunjimi mai shekaru 57, a matsayin wanda zai gaji Madehin a muƙamin. An naɗa shi ne bayan cin jarrabawar da wani kwamiti ya yi masa gami da tattaunawa…
Read More

Majalisar Zartarwa ta amince da biliyan N507 na aikin titin Abuja zuwa Kano

Daga BELLO A. BABAJI Majalisar Zartarwa ta Tarayyar (FEC), ta amince da Naira biliyan 507 da aka ware domin gudanar da aikin sashi na biyu na titin Abuja-Kaduna da Zariya-Kano mai tsawon kilomita 164. Ministan Ayyuka David Umahi ya bayyana hakan a ranar Litinin, bayan kammala zaman majalisar ƙarƙarshin jagorancin Shugaba Bola Tinubu a Fadar Shugaban ƙasa dake Abuja. Ministan ya ce, kuɗin wani ɓangare ne na Naira biliyan 733 da aka ware don ayyukan titina a shiyyoyin Nijeriya. Haka kuma, FEC ta amince da biliyan N24 na aikin gadar Abakpa a Jihar Enugu wanda ke iyaka da rukuni na…
Read More