Babaji

5706 Posts

Boko Haram sun yi garkuwa da farfesa da fasinjoji a hanyar Damaturu zuwa Biu, sun kashe wasu

Daga BELLO A. BABAJI Wasu ƴan ta'adda da ake kyautata zaton ƴan Boko Haram/ISWAP ne, sun sace Farfesa Abubakar El-Juma na Jami'ar Sojoji ta Biu (NAUB) tare da wasu fasinjoji. Lamarin ya auku ne a ranar Lahadi a yankin ƙauyen Kamuya, wanda ke da nisan kilomita 10 tsakanin sa da Buratai, garin tsohon shugaban Sojojin ƙasa, Laftanal Janar Tukur Yusuf Buratai (mai ritaya). El-Juma shine Shugaban Tsangayar nazarin Injiniyanci, wanda kuma yana ɗaya daga cikin waɗanda ake sa ran ba su muƙamin shugaban jami'ar. Rahotanni da dama sun tabbatar da cewa irin haka ya sha faruwa a hanyar, wadda ake…
Read More

Abinda ya sa na yi murabus a matsayin Kakakin Majalisar Dokokin Legas – Meranda

Daga BELLO A. BABAJI Da farko, Blueprint ta ruwaito cewa Meranda Mojisola ta yi murabus daga muƙamin, yayin da Mudashiru Obasa ya sake zama Kakakin Majalisar. A wani jawabi da ta fitar a ranar Litinin, Meranda ta ce ta yi hakan ne don cigaba da kare martabar Majalisar Dokokin. A ranar 13 ga watan Junairu, 2025 ne Meranda ta zama Kakakin, wanda hakan ya haifar da cecekuce da rikici acikin ƴaƴan majalisar da yin barazana ga haɗin-kan mambobinta. Ta ce, ta sadaukar da jagorancin ne don kashe wutar shugabancin majalisar da la'akari da maslahar al'umma. Ta kuma ce, rashin yin…
Read More

CNP ta koka kan ɗalibar da ta rasu a hannun ƴan bindiga

Daga BELLO A. BABAJI Ƙungiyar Masu kishin Arewa ta CNP, ta koka tare da alhinin mutuwar wata ɗalibar Jami'ar Tarayya ta Gusau dake Jihar Zamfara, wadda ta rasa ranta a hannun ƴan bindiga. Ɗalibar mai suna Zarah Abubakar Shehu mai shekaru 21, an sace ta ne tare da ƴan uwanta a ranar 3 ga watan Nuwamba, 2024. Bayan shafe watanni huɗu a hannun ƴan bindigar ne, cikin rashin tausayi ta rasa ranta a hannunsu. A wata sanarwa da Sakataren yaɗa labarai na CNP, Genshak W Wuseli Golak ya fitar, ƙungiyar ta ce ta yi jimamin rashin matashiyar a sanadiyyar gazawar…
Read More

Birgediya Kunle ya zama sabon shugaban NYSC

Daga BELLO A. BABAJI Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Birgediya Janar Kunle Nafiu a matsayin sabon Darakta-Janar na Hukumar kula da Ɗalibai Masu yi wa ƙasa Hidima, wato NYSC. Kafin naɗinsa, Birgediya Kunle shi ne shugaban ma'aikatan Shugaban Sojojin ƙasa, Janar Olufemi Oluyede. Sabon shugaban hukumar, mamba ne na ƴan zangon karatu na 47 na sojojin Nijeriya, kuma jami'in 'Artillery' ne da yayi karatu a Kwalejin Sojoji da Kwalejin Koyon Yaƙi dake Amurka. Haka kuma, ya riƙe muƙamin Daraktan Ma'aikata a Kwalejin Koyon Yaƙi ta Nijeriya. Birgediya Janar Kunle ɗan asalin garin Ileogbo ne dake Ƙaramar Hukumar Aiyedire a Jihar…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Obasa ya koma Kakakin Majalisar Dokokin Legas bayan Meranda ta yi murabus

Daga BELLO A. BABAJI An sake zaɓar ɗan majalisa da ke wakiltar mazaɓar Agege ta 1, Mudashiru Obasa a matsayin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Legas. A ranar Litinin ne aka sake zaɓar sa, biyo bayan murabus da Mojisola Meranda ta yi daga muƙamin. An zaɓi Obasa ne bayan goyon baya da ya samu daga tsohon jagoran mafiya rinjaye na majalisar, Noheem Adams da ke wakiltar Eti-Osa ta 1. Hallau a ranar ce Miranda ta sauka daga muƙamin, inda kuma ƴan majalisar suka zaɓe ta a matsayin mataimakiyar kakakin majalisar. Miranda ta ce, ta yi hakan ne don kare martabar majalisar,…
Read More

ILO ta horar da masu ruwa da tsaki kan tsaron sana’o’i da kawar da bautar da ƙananan yara aikin haƙar ma’adinai

Daga BELLO A. BABAJI A kokarinsu na ganin an kawo ƙarshen bautar da ƙananan yara da ake yi a Nijeriya, Ƙungiyar da ke kula da Manya da Ƙananan wuraren hakar Ma'adinai ba bisa ƙa'ida ba (ILO), ta gudanar da taro daga ranar 18 zuwa 27 ga watan Fabrairu na 2025 a jihohin Neja da Osun. Manufar taron dai ita ceƙarfafa gwiwar masu ruwa da tsaki tare da wakilai daga cikin gwamnati, ma'aikata daga ƙungiyoyi tare da shugabannin yankunan domin kawo ƙarshen aikin bautar da ƙananan yara da ake yi a wuraren. Hakazalika, an bai wa mambobin kwamitin da ke sanya…
Read More

Kotun Ɗaukaka ƙara ta ƙi amincewa da buƙatar hana jami’an gwamnati zuwa ƙasashen waje neman magani

Daga BELLO A. BABAJI Kotun Ɗaukaka ƙara ta Jihar Legas ta ƙi amincewa da buƙatar babban lauyan Nijeriya (SAN), Femi Falana, na haramta wa jami'an gwamnati zuwa ƙasashen waje neman magani. Ta ce, hakan wani nau'i ne na tauye haƙƙin ɗan-adam da dokar ƙasa ta bayar na amince wa jami'an gwamnati da waɗanda ba su ba zuwa ƙasashen waje neman magani. A watan Yulin 2010 ne Falana ya maka Gwamnatin Tarayya a kotu inda ya ke neman a tabbatar da samar wa al'umma asibitoci da sauran wuraren kula da lafiya masu inganci da kayan aiki isassu domin kula da lafiyarsu,…
Read More

Gwamnan Ribas ya bada sabon umarni bayan hukuncin Kotun Ƙoli kan ƙananan hukumomi

Daga BELLO A. BABAJI Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya ce za a sake gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin jihar. Hakan ya biyo bayan rushe zaɓen ne da Kotun Ƙoli ta yi, wanda aka gudanar a ranar 5 ga watan Oktoba, 2024. A wata hira da gidan talabijin, Fubara ya tabbatar wa al'umma cewa gwamnatinsa za ta bi umarnin doka. Don tabbatar da ƙananan hukumomin sun cigaba da aiki yadda ya kamata, gwamnan ya umarci Jagororin Hukumar Ƙananan Hukumomi ta jihar da ta karɓe iko a ƙananan hukumomi 23 dake jihar, waɗanda za su yi hakan ne a matsayin riƙon…
Read More

Magidanci ya yi sanadin mutuwar matarsa bayan zane ta kan abincin buɗe baki

Daga BELLO A. BABAJI Rundunar ƴan sandan Jihar Bauchi ta ce ta kama wani mai suna Alhaji Nuru Isa ɗan shekara 50 bisa tuhumar sa da amfani da bulala wajen zane matarsa mai suna Wasila Abdullahi, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwarta. Lamarin ya faru ne a kusa da makarantar kwalejin mata da ke Unguwar Fadaman Mada a jihar. Kakakin rundunar, CSP Ahmed Wakil a wata takarda da ya fitar a ranar Lahadi, ya ce sun samu rahoton aukuwar lamarin ne da misalin ƙarfe 11:30 na dare a ranar 1 ga watan Maris. Ya kuma ce, al'amarin ya biyo bayan…
Read More

Tsohon ɗan wasan Arsenal, Ozil ya shiga siyasa

Daga BELLO A. BABAJI Tsohon tauraron kwallon kafa, Mesut Ozil, ya shiga harkar siyasa a Turkiyya bayan da ya samu kujera a babban kwamitin jam'iyya mai mulki ta ƙasar. An zaɓi Ozil ne a yayin babban taron jam'iyyar a birnin Ankara a ranar Asabar, wanda hakan ke ƙara nuna karfin alaƙar da ke tsakanin sa da Shugaba Recep Tayyip Erdogan. Ozil mai shekaru 36, ya samu ƙarin kusanci da Erdogan ne a shekarar 2019, a lokacin da ya auri tsohuwar wacce ta fi kowa kyau a Turkiyya, Amine Gulse, wanda hakan ya zama ɗaya daga cikin dalilansa na shiga siyasa.…
Read More