02
Mar
Daga BELLO A. BABAJI Ministan Wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ya alƙawarin cewa za a samu isasshen wutar lantarki a watan Ramadan wanda aka fara a ranar Asabar. A saƙonsa ga al'ummar Musulmi, Ministan ya ce yana sane da ƙalubalen da ƴan Nijeriya suke fuskanta kan rashin wadatacciyar wutar lantarki. Ya ce, lallai musulmai suna buƙatar ƙarin adadin lantarki acikin watan azumi, wanda a saboda haka ne suke ƙoƙarin samar da isasshen wutar a yanzu da ma nan gaba. Ya kuma ce, Gwamantin Tarayya tana ƙoƙarin shawo kan matsalolin ɗaukewar wuta a sakamakon lalacewar rumbun lantarki na ƙasa tare da ake…
