01
Mar
Daga BELLO A. BABAJI Hukumar Tattara Kuɗaɗen Haraji ta Birnin Tarayya, FCT-FIRS, ta yi barazanar tilasta wa waɗanda basa son biyan haraji tarar N500,000 a Abuja. Shugaban riƙon ƙwarya na hukumar, Michael Ango ya bayyana gargaɗin a ranar Alhamis a Abuja, a lokacin gangamin wayar kan al'umma game da biyan haraji da aka saba yi duk shekara. Ya ce, duk waɗanda ba su biya harajin 2024 ba zuwa Junairun 2025, za a sanya masu tarar N500,000 a matsayin horo. Ango ya ce, a lokacin da suka sanya wa'adin 31 ga watan Junairu, 2025, an samu kamfanoni da dama da suka…
