Babaji

5706 Posts

Rundunar Sojojin ƙasa ta ninka wa dakaru kuɗin alawus na abinci

Daga BELLO A. BABAJI Shugaban Sojojin ƙasa, Laftanal Kanal Olufemi Oluyede ya sanar da ƙari a kuɗin abinci ga jami'ansu, wanda daga N1,500 ya koma N3,000 a kullum. Daga ƙarshen watan Maris ne za a ƙaddamar da ƙarin ga dakarun. Ya bayyana haka ne a ranar Laraba, a lokacin da ya ke gabatar da jawabi ga jami'an runduna ta 81 a Filin Faretin Birget na 9 dake Ikeja a Jihar Legas. Shugaban sojojin ya koka ga yadda ake bai wa jami'an N1,500 a matsayin kuɗin abinci na kowacce rana, ya na mai tabbatar masu da ƙoƙarinsa na inganta walwalarsu. Ya…
Read More

Ƙara farashin kira zai sa a samu ingancin sabis – Minista

Daga BELLO A. BABAJI Ministan Sadarwa da Fasahar Zamani, Dakta Bosun Tijani ya ce ƙarin kaso 50 da kamfanonin Telekom suka yi zai taimaka wajen samun ingantaccen sabis ga ƴan Nijeriya. Ministan ya bayyana haka ne wa manema labarai a Fadar Shugaban ƙasa, ranar Alhamis. Ministan ya jagoranci tawagar kamfanin Bharti Airtel ƙarƙashin jagorancin Shugabansa, Sunil Mittal a wata ganawa da Shugaba Bola Tinubu. Dakta Bosun ya ce, hukuncin karin farashin ya zama dole ganin yadda gwamnati take ƙoƙarin samar da maslaha a tsakanin al'umma da kamfanonin. Ya ƙara da cewa, gwamnati ta amince da ƙarin farashin ne don guje…
Read More

Rundunar ƴan sanda ta fara gwajin lafiya ga kuratan da aka ɗauka a 2022

Daga BELLO A. BABAJI Rundunar ƴan sandan Nijeriya ta fara gudanar da gwajin ƙwaƙwalwa ga masu neman aikin kurtun ɗan sanda na shekarar 2022 a cigaba da aikin tantancewa. A ranar 26 ga watan Fabrairu ne aka fara aikin wanda kuma za a kammala a ranar 12 ga watan Maris a rukuni 17 na rundunar dake faɗin Nijeriya. Jami'in yaɗa labaran rundunar, Olumuyiwa Adejobi ya bayyana hakan a wata takarda, inda kuma ya yi kira ga masu neman aikin da su duba shafukan yanar gizo ta adireshin da suka nemi aikin don ganin matakin da suke tare da cire kwafin…
Read More

Kaduna: Sojojin sama sun tabbatar da mutuwar fararen hula da umartar a yi bincike

Daga BELLO A. BABAJI Rundunar Sojojin sama ta fara gudanar da bincike game da lamarin da ya yi sanadin mutuwar jami'inta da wasu fararen hula a Unguwar Gangare dake Barakallahu a Jihar Kaduna. Lamarin ya kuma sabbaba jikkata wasu da dama. Daraktan yaɗa labaranta, AVM Olusola Akinboyewa ya tabbatar da al'amarin, inda ya ce ana bai wa waɗanda suka samu raunuka kula a Asibitin 461 NAF na rundunar. Rundunar ta koka game da rashin da aka yi tare da jajenta wa iyalan waɗanda suka rasa rayukansu a yayin iftila'in. Ya kuma tabbatar masu da cewa za a gudanar da ƙwaƙƙwaran…
Read More

Natasha ta nemi a tafka mahawarar binciken ta a bainar jama’a

Daga BELLO A. BABAJI Sanatar da ke wakiltar Jihar Kogi ta Tsakiya a Majalisar Dattawa, Natasha Akpoti-Uduaghan ta haƙiƙance akan sai dai a gudanar da binciken ta ta hanyar haska wa al'umma kai-tsaye. Ta ce, ƴan Nijeriya suna da ƴancin su shaida al'amarin. A wani saƙo da aka wallafa a ranar Alhamis ta soshiyal mediya, Natasha ta ce da farko an hana ta magana a fili game da batun da wasu batutuwan majalisar, amma yanzu ta zaɓi ta bayyana wa al'umma. Ta yi kira ga ƴan Nijeriya da su bibiyi al'amarin don tabbatar da an yi adalci. Ta kuma wallafa…
Read More

An kusa fara cin moriyar gidauniyar Dala miliyan 200 ga masu fasahar ƙirƙira – Hannatu Musawa

Daga BELLO A. BABAJI A ranar 1 ga watan Yuni ne Nijeriya za ta fara amfani da Dala miliyan 200 na Gidauniyar bankin Afrexim wajen bunƙasa ayyukan walwala da jin-daɗi da da fasahar ƙiƙira a harkar tattali. Ministar Al'adu, Hannatu Musa Musawa ta faɗi hakan a ranar Laraba, inda ta ce suna ƙoƙarin amfani da Dala biliyan 2 wajen zuba jari a wasu ƙasashe da ma cikin gida Nijeriya, ta yadda za a samar da ayyukan yi da kuma faɗaɗa harkar tattali a zamanance zuwa Dala biliyan 100 nan da shekarar 2030. A wata sanarwa da Ma taimaka mata kan…
Read More

Gwamnatin Katsina ta ɗauki mutane 34,000 aiki a jihar

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina A cikin shekara biyunta na farko, gwamnatin Jihar Katsina ta ɗauki mutane 34,000 aiki a fannoni daban-daban a faɗin jihar. Gwamna Dikko Raɗɗa ya faɗi haka a wajen bikin bada tallafin kuɗi ga mata 600 domin inganta kiwo a ƙarƙashin Gidauniyar Kabir Magaji Gafiya a garin Kaita. Gwamnan, wanda ya samu wakilcin Mataimakinsa, Malam Farouk Lawal Joɓe, ya ce babu wata gwamnati a ƙasar nan da ta ɗauki adadin waɗannan mutane aiki. Hakan ya nuna ƙoƙarin gwamnatin Raɗɗa na rage adadin rashin aikin yi da kuma inganta rayukan al'ummar jihar, acewar mataimakin. Ya kuma ce,…
Read More

Gwamnatin Kano ta horar da jami’an labarai dabarun sadarwar na zamani

Daga BELLO A. BABAJI Kwamishinan Labarai da Harkokin Cikin gida na Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya jaddada ƙoƙarin gwamnatin jihar na bunƙasa ƙwarewa a harkar yaɗa labarai. Waiya ya bayyana hakan ne a lokacin buɗe taron ƙara wa juna sani na kwana uku game da dabarun aiki ga jami'an labarai daga ma'aikatu da ɓangarori da hukumomi da kuma daga ƙananan hukumomi. Ma'aikatar ta shirya taron ne da haɗin-gwiwar Cibiyar Hulɗa da Jama'a ta Ƙasa (NIPR) reshen jihar. A wata sanarwa da Daraktan Ayyuka na Musamman na Ma'aikatar, Sani Abba Yola ya fitar, ya ce Waiya ya jinjina wa Gwamna Abba…
Read More

Buhari da El-Rufa’i da Amaechi sun ƙaurace wa taron jagororin APC

Daga BELLO A. BABAJI Jagororin APC a mataki na ƙasa sun taru a Sakatariyar jami'yyar dake Abuja domin gudanar da taron kwamitin majalisar zartarwa (NEC). Jami'an tsaro sun cike hanyoyin dake kai wa zuwa ga sakatariyar waɗanda suka haɗa da sojoji da jami'an Guards Brigade, inda aka taƙaici zirga-zirgar ababen hawa da na mutane. Wasu daga cikin waɗanda suka halarci taron da wuri sun haɗa da tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Abdul'aziz Yari da Ministan Kasafi, Atiku Bagudu da Mataimakan Kakakin Majalisar Wakilai, Benjamin Kalu. Sauran sun haɗa da Gwamnonin Jihohin Edo, Benue, Ondo, Ekiti, Kaduna, Jigawa, Nasarawa, Yobe, Neja, Legas,…
Read More

Bashin Nijeriya na Bankin Duniya zai iya kai wa tiriliyan N13.7 idan Tinubu ya ciyo N3.34trn

Daga BELLO A. BABAJI Ana hasashen bashin Nijeriya a Bankin Duniya ka iya ƙaruwa da Dala biliyan 9.2 matuƙar Shugaba Bola Tinubu ya ciyo bashi guda shida da adadinsu ya kai Dala biliyan 2.23 a shekarar 2025 da ya ke shirin yi. Hakan na nuna yadda ƙasar ke cigaba da dogaro da bashi don tallafa wa manyan ɓangarori harkar tattali waɗanda suka haɗa da lafiya da ilimi da sauran su. A shekarar 2023 ne Bankin Duniya ya amince da bai wa Nijeriya bashin da Dala biliyan 2.7 don gudanar da ayyukan samar da makamashi, ilimi da lantarki. Daga cikin shirye-shiryen…
Read More