Babaji

5706 Posts

Babu shirin cire Ganduje, yayin da El-Rufai ya ƙaurace wa taron jagororin APC

Daga BELLO A. BABAJI Shugabancin jam'iyyar APC ya yi watsi da zargin da ake yi na cewa akwai yiwuwar Shugaba Bola Tinubu ya nemi Abdullahi Umar Ganduje da ya yi murabus daga kujerar jagorancin jam'iyyar a zaman jagororinta a Abuja, ranar Laraba. Sakataren jam'iyyar, Sanata Ajibola Basiru ya bayyana hakan a yayin hira da ƴan jarida, inda ya bayyana zargin a matsayin ƙirƙirarre da ba shi da tushe. Ya ce, zaman nasu ba zama ne na zaɓe ba, wanda sun so gudanarwa tun wata Satumbar 2024, don haka babu maganar sauke Ganduje ko neman ya yi murabus. Sanatan ya kuma…
Read More

Gwamnatin Sokoto za ta kashe miliyan N998 a shirin ciyarwa na Ramadan

Daga BELLO A. BABAJI Gwamnatin Jihar Sakkwato ta ce za ta kashe kimanin Naira miliyan 998 a shirin ciyarwa a yayin azumin watan Ramadana na shekarar 2025. Za a gudanar da shirin ne a cibiyoyi 155 dake sassan jihar. A lokacin da ya ke magana a yayin raba kayan abinci ga manajojin cibiyoyin, Gwamna Aliyu Ahmad ya ce za a bai wa kowacce cibiya ɗanyen abinci kala-kala da kayan girke-girke. Ya ce, mutane 1,400 aka ɗauka a matsayin waɗanda za su gudanar da ayyukan ciki har da mata masu girki guda 610. Ya kuma ce, za a riƙa ciyar da…
Read More

Ka daina yi kamar ƙaramin yaro don ba a ba ka minista ba – Fadar Shugaban ƙasa ga El-Rufa’i

Daga BELLO A. BABAJI Kakakin Shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya shawarci tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i da ya daina nuna halin yara kaɗai saboda bai samu muƙamin minista ba. Da farko dai, Shugaba Tinubu ya sanya sunan El-Rufa'i acikin waɗanda aka so bai wa minista a gwamnati, wanda daga bisani Majalisar Dattawa a yayin tantancewa ta cire shi. Daga lokacin ne El-Rufa'i ya zama ƙarfen ƙafa ga Gwamnatin Shugaba Tinubu da jami'iyyar APC ta hanyar soka da wasu ayyuka na nuna fushi. A kwanan nan ne aka yi hira da El-Rufa'i, a inda ya yi ikirarin cewa ba…
Read More

Ayyukana su ne a gabana, ba mayar da martani ba – Ribaɗu ga El-Rufa’i

Daga BELLO A. BABAJI Mai bai wa Shugaban ƙasa Shawara kan harkar Tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribaɗu ya ƙaryata kalaman tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i, na cewa yana shirin ɓata masa suna saboda burinsa (Ribaɗu) na tsayawa takara a zaɓen shekarar 2031. A wata hira da aka yi da El-Rufa'i ta gidan telebijin na Arise a ranar Litinin, ya zargi Ribaɗu da haɗa kai da Gwamna Uba Sani na Kaduna da Hukumar Hana Rashawa da Laifuka masu Kama da ita (ICPC) don ɓata masa suna a idon al'umma. Saidai, a wata takarda daga ofishin Ribaɗu da aka fitar…
Read More

Sirikar Ministan Labarai ta rasu

Daga BELLO A. BABAJI Hajiya Hauwa Yakub Usman, wadda sirika ce ga Ministan Labarai da Wayar kan al'umma, Mohammed Idris, ta rasu tana da shekaru 70 a duniya. An yi mata sallar jana'iza ne a babban masallacin ƙasa, wato National Mosque dake Abuja, inda kuma aka binne ta a maƙabartar unguwar Gudu a birnin. Manyan jami'an gwamnati ne suka halarci jana'izarta waɗanda suka haɗa da Mai bai wa Shugaban ƙasa Shawara kan harkar tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribaɗu; Ministan Kasafi da Shirya Tattali, Sanata Atiku Bagudu; da wasu daga cikin jami'an Ma'aikatar Labarai da daraktocin hukumomin gwamnati da dai sauransu.…
Read More

Ana dab da yin sabon ƙidaya a Nijeriya bayan Shugaba Tinubu ya kafa kwamiti

Daga BELLO A. BABAJI Ana cigaba da shirye-shirye na fara gudanar da sabon ƙidaya a Nijeriya tun da aka yi na ƙarshen a watan Nuwamban shekarar 2006. A yayin ganawa da jami'an Hukumar Ƙidaya ta Ƙasa (NPC) a Fadar Shugaban ƙasa dake Abuja, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce zai kafa kwamiti ne da zai haɗa kasafin ƙidayar da yanayin tattalin arziƙin ƙasa don su dace wajen tafiyar da aikin. Ya ce, daga cikin tsare-tsaren akwai sanya Hukumar Katin Ɗan ƙasa (NIMC) a matsayin ɗaya cikin ɓangarorin da za su bada gudunmawa wajen gudanar da aikin. Ya kuma jaddada ƙoƙarinsa…
Read More

Wata sabuwa: NNPP ta dakatar da Sanata Sumaila da ƴan Majalisar Wakilai uku a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Jam’iyyar NNPP mai mulkin jihar Kano ta dakatar da wasu manyan mambobin guda hudu da suka hada da Sanata Kawu Sumaila, Ali Madakin Gini, Sani Abdullahi Rogo, da Kabiru Alhassa Rurum, bisa zarginsu da yiwa jam’iyyar zagon kasa. Blueprint Manhaja ta rawaito shugaban jam’iyyar na jihar Kano Hashimu Suleiman Dungurawa ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano. Dungurawa ya ce an zaɓi wadannan ‘yan majalisar dokokin ne a ƙarƙashin jam’iyyar NNPP amma a kwanakin baya suna yin wasu abubuwa da suka saba da Manufofi da akidar jam’iyyar. Kazalika ya…
Read More

An rufe Jami’ar FUDMA bayan kashe wani ɗalibi

Daga UMAR GARBA a Katsina Hukumomi a Jami’ar gwamnatin tarayya ta Dutsinma (FUDMA) da ke Jihar Katsina, sun rufe makarantar, sakamakon zanga-zangar da ta ɓarke a jami'ar bayan da jami'an tsaron haɗin-gwiwa na Civilian Task Force suka harbe wani ɗalibi da ke ajin ƙarshe ( Level 400) a jami'ar. Rahotanni sun bayyana cewa jami’an Civilian Task Force sun harbi wasu ɗalibai biyu bisa tunanin 'yan bindiga ne, lamarin da ya yi sanadin mutuwar xaya daga cikinsu. An harbe Sai’d Abdulkadir, ɗalibi da ke karatun digiri a fannin aikin noma, bayan da abokinsa ɗalibi ya goya shi akan babur. Majiyar Blueprint…
Read More

Majalisar Limaman Juma’a ta jinjina wa Gwamnatin Kano bisa tantance ƙungiyoyin da ba na gwamnati ba

Daga BELLO A. BABAJI Majalisar Limaman Juma'a ta Ƙasa, ƙarƙarshin jagorancin Shaikh Muhammad Nasiru Adam, ta bayyana cikakken goyon bayanta ga Gwamnatin Jihar Kano bisa shirinta na tantance ƙungiyoyn da ba na gwamnati ba. Malamin ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, a yayin ganawa da manema labarai a Kano, inda ya ce hakan abu ne mai muhimmanci ga al'umma da ma jihar baki ɗaya. Ya ce, ayyukan wasu ƙungiyoyi sun ci karo da al'adu da addinan mutanen Kano waɗanda su kan yin munanan tasiri a gare su, don haka ya ke da muhimmanci a tantance su. Shugaban ya kuma…
Read More

An yi garkuwa da tsohuwa a asibitin mahaukata na Dawanau a Kano

Daga BELLO A. BABAJI Wasu da ake zargin masu satar mutane ne sun yi garkuwa da wata tsohuwa mai shekaru 60 a Asibitin Mahaukata na Dawanau dake ƙaramar hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano. Lamarin ya auku ne a lokacin da matar mai suna Talatu Ali ke wajen jiran likita domin duba lafiyar ƙwaƙwalwarta. Wani ƙwararren mai sharhi akan daƙile ayyukan ta'addanci, mai suna Zagazola Makama ya ce ɗanta mai suna Nasiru Aliyu da wani Aliyu Garba wanda ƙani ne a wajenta, suka kai ta asibitin a ranar 19 ga watan Fabrairu. A lokacin da suke jiran ganin likita ne…
Read More