24
Feb
Daga BELLO A. BABAJI Majalisar Dattawa ta fara gudanar da zama na kwanaki biyu don jin ra'ayoyi game da ƙudirin dokar gyaran haraji, inda ta haɗa masu-ruwa-da-tsaki daga ɓangaren harkokin tattali da kuɗi. Waɗanda suka halarci zaman sun haɗa da Ministan Kuɗi da Tattali, Wale Edun; Shugaban Hukumar Tattara Kuɗaɗen Haraji (FIRS), Zacch Adedeji; Shugaban Kamfanin Man fetur na Ƙasa (NNPCL), Mele Kyari; Mambobin Majalisar Zartarwa da jagororin wasu hukumomi da sauransu. Shugaban kwamitin majalisar akan kuɗaɗe, Sanata Sani Musa ya tabbatar da cewa za a gudanar da zaman cikin tsari kuma bisa gaskiya da adalci tare da la'akari da…
