
Daga BELLO A. BABAJI
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da kan al’umma, Mohammed Idris, ya yi tsokaci game da alaƙa mai ƙarfi da ke tsakanin addini da siyasa da mulki wajen samar wa Nijeriya ci-gaba.
Mai taimaka masa kan yaɗa labarai, Ibrahim Rabi’u a wata sanarwa, ya ce Ministan ya bayyana hakan ne a ranar Asabar a Kaduna, yayin gabatar lakcar shekara-shekara da gidan talabijin na NTA da Hukumar Kula da gidajen Rediyo ta Ƙasa (FRCN) da Hukumar VON (Voice of Nigeria) suka saba shiryawa.
Ministan ya yi magana ne akan maudu’in shigar malamai harkokin siyasa da tasirin sa ga ƙasa da al’umma, inda ya ce lallai sai an haɗa ababe ukun a yayin samar da ci-gaba la’akari da tarihi a jiya da yau da kuma hasashen nan gaba.
Ya ce, kamar yadda akan samu sauye-sauye a addini, siyasa da mulki, haka ma irin haka na samuwa a harkokin siyasar cikin gida da ta waje a yayin sauya yadda al’umma ke kallon haɗin kan ƙasa.
A jawabinsa game da muhimmancin watan Ramadan, Idris ya yi kira ga ƴan Nijeriya da su yi amfani da damar watan wajen ƙarfafa haɗin kan da ke tsakanin su da ƙoƙarin ciyar da ƙasa gaba.
Ya kuma yaba wa Shugaba Bola Tinubu kan sanya hannu a kasafin 2025 da adadinsa ya kai Naira tiriliyan 54 da zai fifita harkokin tsaro, ilimi, lafiya, noma da ababan more rayuwa, waɗanda za su taimaka wajen samar da ci-gaba mai ɗorewa a Nijeriya.