Babaji

5704 Posts

Ƙungiyar goyon bayan Shugaba Tinubu ta naɗa Yahaya Bello a matsayin babban tauraro

Daga BELLO A. BABAJI Ƙungiyar goyon bayan Shugaba Tinubu ta (NTCA), ta naɗa toshon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a matsayin babban tauraro a tafiyarsu. NTCA, wadda ke da mambobi a gida Nijeriya da ma ƙasashen waje, ta na ƙoƙari ne wajen ɗaukaka ayyukan Shugaba Bola Tinubu da ke ƙunshe da inganta harkokin tattalin arziƙi da siyasa a ƙasar. Waɗanda suka gabatar naɗin ga tsohon gwamnan sun haɗa da Kodinetan ƙungiyar, Hon. Henry Nwabueze da Shugaban Wayar da kai, Dakta Haruna Madisca. A sanarwar da ta fitar, ta ce ta naɗa Yahaya Bello, wanda aka fi sani da 'The White…
Read More

Zargin Cin zarafi: Akpabio da Natasha za su gurfana gaban Kwamitin Majalisar Dattawa

Daga BELLO A. BABAJI Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan za su gurfana a gaban kwamitin ladabtarwa na majalisar don yi masu hukunci bisa zargin cin zarafi. Mataimakin Mai Tsawatarwa na majalisar, Onyekachi Nwebonyi a wata hira da gidan talabijin na 'channels', ya ce waɗanda lamarin ya shafa za su yi wa kwamitin bayani game da abinda suka sani akan zargin cin zarafin, wanda Natasha ta ɗora wa Akpabio. Ya ce, za su yi hakan ne don bai wa kowane ɓangare damar gabatar da hujjojinsa. Natasha, wadda ke wakiltar Jihar Kogi ta Tsakiya, a ranar 28 ga…
Read More

Shettima ya nemi a riƙa taya Shugaba Tinubu aikin gyaran fuskar da ya ke yi wa Nijeriya

Daga BELLO A. BABAJI A ranar Laraba ne Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya yi kira ga haɗin kai tsakanin jagorori wajen tallafa wa ƙoƙarin Shugaba Bola Tinubu na yin gyaran fuska a Nijeriya. Shettima ya yi kiran ne a yayin taron shan ruwa da Shugaba Tinubu ya jagoranta a Fadar shugaban ƙasa, wanda aka gayyaci jagororin Majalisar Dattawa. Ya ce, Nijeriya ta kai matakin da jagorancin Shugaban ƙasar da tsare-tsarensa sai sun samu aiwatarwa bisa inganci domin samun sauyi mai ɗorewa, ya na mai cewa ƴan Nijeriya sun fara ganin alfanon haka a saukar farashin abinci da fetur da…
Read More

Ramadan: Rundunar ƴan sandan Kano ta tabbatar da haramta tashe a jihar

Daga BELLO A. BABAJI A ƙoƙarinta na daƙile ayyukan ta'addancin ƴan daba, rundunar ƴan sandan jihar Kano ta jaddada batun haramta yin tashe da aka saba yi a kowane Ramadan a jihar. Gwamnatin jihar ta yi hukuncin ne domin inganta kula da rayuka da dukiyoyin al'umma yayin da ɓata-gari suke amfani da hakan wajen farmakar mutane a gidajensu. Rundunar ta gudanar da zama na masu-ruwa-da-tsaki a unguwanni don tattauna hanyoyin da za a bi wajen daƙile harin ɓata-garin. Haka kuma, an bayyana shan miyagun ƙwayoyi a matsayin musabbabin samuwar harkar dabanci a jihar. A sanarwar da Kakakinta, SP Abdullahi Haruna…
Read More

Direba ya murƙushe ƙaramar yarinya yayin tsere wa jami’an ‘taskforce’

Daga BELLO A. BABAJI Wasu jami'an kula da zaman lafiyar al'umma a Edo, sun yi taƙaddama da wani direban motar kasuwa a Birnin Benin dake jihar, wanda hakan ya yi sanadin mutuwar wata ƙaramar yarinya. A yammacin ranar Laraba ne al'amarin ya faru a titin 'Ring Road'. Ya auku ne a lokacin da wani jami'in taskforce ya tunkari direban a salo na firgitawa bisa saɓa wa dokar hanya, inda jami'in ya yi ƙoƙarin kutsawa cikin motar. Ganin yadda suka yi ƙoƙarin riƙe kan motar ya sanya direban fizgar motar a guje, wanda hakan ya sa ya rasa makama tare da…
Read More

Majalisar Wakilai ta amince da ƙudirin dokar haraji da warware matsalolin VAT

Daga BELLO A. BABAJI A ranar Alhamis ne Majalisar Wakilai ta amince da ƙudiri guda huɗu na neman gyaran fuska ga dokar haraji a Nijeriya da Shugaba Bola Tinubu ya gabatar. A lokacin da ya ke gabatar da rahoton nazari akan ƙudirin, Shugaban kwamitin majalisar kan kuɗi kuma jagoran kwamitin tantance ƙudirin, James Faleke, ya ce sun gudanar da aikin tantancewa mai zurfi tare da warware matsalolin da suka jefa al'umma cikin damuwa a karon farko da aka gabatar da shi. Ya ce, an warware batutuwan da suka haifar da cecekuce game da abinda aka tara daga harajin VAT da…
Read More

Titin Legas zuwa Kalabar aiki ne abin alfahari nan gaba – Fadar Shugaban Ƙasa ga Obasanjo

Daga BELLO A. BABAJI Gwamnatin Tarayya ta ce aikin babban titin Legas zuwa Kalabar da zai lanƙwame Naira tiriliyan 15.6 abu ne da zai bada damar bunƙasa tattalin arziƙi a ɓangarori daban-daban ga ƴan Nijeriya. Bayanin ya biyo bayan tsokacin toshon Shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, wanda ya bayyana aikin a matsayin albazzaranci ga dukiyar ƙasa. Saidai, a yayin kare batun a wata hira da tashar TVC, Mai taimaka wa Shugaba Bola Tinubu akan Harkokin Sadarwa, Sunday Dare, ya ce aikin zai zama ɗaya daga cikin manyan ayyukan da wani shugaba ya taɓa yi a Nijeriya. A sashi na shida na…
Read More

Masarautar Kano: Kotun Ɗaukaka ƙara ta dakatar da aiwatar da hukuncin tabbatar da Sarki Sanusi

Daga BELLO A. BABAJI A wani sabon al'amari game da rikicin Masarautar Kano, Kotun Ɗaukaka ƙara a Abuja, ta janye hukuncinta na ranar 10 ga watan Junairu, wanda ya amince da gyaran dokar majalisar masarautar Kano da Gwamnatin jihar ta yi, har zuwa lokacin da Kotun Ƙoli za ta yi hukunci. Kotun Ɗaukaka ƙara a Kano ta jingine umarnin ranar 20 ga watan Yuni da Alƙali Abubakar Liman na Babbar Kotun Tarayya dake Kano ya yi na soke matakan da gwamnatin jihar ta bi na yin kwaskwarima ga dokar majalisar masarautar Kano ta 2024 da kuma naɗa Sarkin Sanusi Lamiɗo…
Read More

Ɗangote ya sake rage farashin fetur

Daga BELLO A. BABAJI Matatar Ɗangote ta rage farashin fetur a defot zuwa Naira 815 a kowacce lita. Hakan ya biyo bayan saukar farashin man ne a inda ake saukewa zuwa N774.82 ga kowacce lita, wanda ya yi ƙasa da na Matatar Ɗangote da ake bayarwa akan N825. Kakakin ƙungiyar ƴan kasuwar fetur masu zaman kansu, Chinedu Ukadike ya tabbatar da ci-gaban. Ragin farashin ya samu ne a yayin hamayya da ake samu kan farashin a tsakanin manyan ƴan kasuwar Albarkatun mai a Nijeriya. A watan baya ne aka sha samun gogayyar farashinsa, inda Matatar Ɗangote da NNPCL suka yi…
Read More

Gwamnatin Tarayya ta ƙulla yarjejeniya da Majalisar Birtaniya don bunƙasa masana’antar ƙirƙira a Nijeriya

Daga BELLO A. BABAJI Ministar Al'adu, Hannatu Musa Musawa, ta ce takardar yarjejeniyar (MoU) da ta sanya wa hannu da Majalisar Birtaniya, an samar da ita ne don haɓaka harkokin al'adu da ƙirƙira gami da ƙarfafa haɗin-gwiwa da ƙasashen duniya. A wani saƙo daga ma'aikatar, Musawa ta bayyana hakan ne a yayin ganawa da wakilan majalisar a ranar Laraba, 26 ga watan Fabrairu, a Legas. Hakan ya biyo bayan haɗewa da Ma'aikatar Walwala ta yi da ta Al'adu da kuma ta Ƙirƙirarren Tattali don bunƙasa harkokin al'adu da tattali a Nijeriya. A lokacin da ta ke jawabi a taron, Musawa…
Read More