Babaji

5704 Posts

Ɓullar wata cuta ta yi sanadin mutuwar ɗaliban jami’a biyar a Kebbi

Daga BELLO A. BABAJI Wata cuta da ba a kai ga sanin haƙiƙanin ta ba a Jihar Kebbi, ta yi sanadiyyar mutuwar wasu ɗalibai guda biyar da ke karatu a Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta jihar dake Aliero (KSUSTA). Wasu ɗaliban da suka buƙaci a ɓoye sunayensu, sun shaida wa manema labarai cewa huɗu daga cikin ɗaliban da suka kamu da cutar sun rasu ne a makon da ya gabata, yayin da ɗayan kuma ya rasu a ranar Lahadi bayan wani zazzaɓi na lokaci guda. Wani shaida ya ce, a makon da ya gabata ne jami'an Hukumar Lafiya ta Duniya…
Read More

Natasha ta bayyana yadda ta kutsa kai zaman Majalisar Dokoki ta Duniya

Daga BELLO A. BABAJI Biyo bayan cecekuce game da dakatar da ita da zuwanta zaman Majalisar Dokoki ta Duniya a New York, Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta bayyana yadda ta ɗauki nauyin tafiyarta ba tare da umarnin Majalisar Dattawan Nijeriya ba. Sanatar ta bayyana hakan ne bayan samu labarin cewa hukumomin tsaro na leƙen asiri suna bincike game da zuwanta zaman, wanda Majalisar Dattawan ta shigar da ƙorafi a kai. Ta ce, ta yi rajista ne ta yanar gizo wanda ya sa aka amince mata zuwa taron, kamar yadda a baya ma haka aka yi a yayin shirya zaman. Ta kuma…
Read More

Nijeriya ta fara bincike kan yadda Natasha ta kutsa zaman Majalisar Dokoki ta Duniya

Daga BELLO A BABAJI Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da bincike akan yadda Sanatar da aka dakatar, Natasha Akpoti-Uduaghan ta samu halartar zaman majalisar dokoki ta Duniya da aka gudanar a New York ba tare da ayyana ta a matsayin wakiliya ta musamman daga Nijeriya ba. Majiya daga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta ce jami'an ƴan sandan farin kaya (DSS) da na Leƙen asiri (NIA) ne suke gudanar da binciken. Haka kuma hukumomin suna bincike akan wanda ya sahale mata, sannan ko ta halarci taron ne don tozarta Nijeriya. Majiyar ta ce, Nijeriya ta na ƙoƙarin kiyaye dokokin shiga IPU waɗanda…
Read More

Yaushe ne lokacin buɗe baki?

Daga ALI ABUBAKAR SADIQ Wannan na ɗaya daga cikin abubuwa da musulmi su ka sami rarrabuwar kai tsawon zamunna a tarihin musulunci zuwa yanzu. Yayin da Ahlul Sunnah ke ajiye azumi bayan faɗuwar rana, ƴan Shi'a kuma sai duhu ya bayyana. Kowanne ɓangare ya na da wata madogara, domin dai Ahlul Sunnah sun kafa hujja da hadisin Bukhari na 1091, wanda aka ruwaito Annabi ya ce, "Idan Rana ta faɗi, lokacin buɗe baki ya yi." Su kuma Yan Shia sai su ka kafa hujja da ayar Ƙur'ani cikin Q17:78 "Ka tsayar da salla a karkatar rãnã zuwa ga duhun dare…
Read More

Ƙarancin fetur: Duk da tsamin dangantaka, Nijar ta roƙi Tinubu mai

Daga BELLO A. BABAJI Jamhuriyar Nijar na neman agajin Nijeriya sakamakon ƙarancin man fetur da ta ke fama da shi duk cewa akwai tsamin dangantaka na tsawon watanni a tsakanin ƙasashen biyu. Rahotanni sun bayyana cewa, wasu manyan jami'an gwamnatin mulkin soji na Nijar sun je Abuja domin ganawa da wakilan Shugaba Tinubu. Bayan tattaunawar ne aka amince da kai wa Nijar tankokin fetur guda 300. Wani babban jami'in gwamnati ya ce, Nijeriya ta amince wa buƙatar takwararta ne don hakan ya zama ɗaya daga cikin jinshiƙan sulhu a tattaunawar da suke yi a tsakanin su. Ya ce, tawagar jami'an…
Read More

Goron Azumi: Shan ORS yayin azumi – Cikakken bayani da illolinsa

Daga CHIROMA AMINU ASID Menene ORS?Oral Rehydration Solution (ORS) haɗin ruwan sha ne da gishiri da sukari wanda ake amfani da shi don maye gurbin ruwa da sinadaran jiki da suka ragu saboda gudawa, amai, ko zafin rana. Ana amfani da shi musamman don hana bushewar jiki (dehydration). Shan ORS yayin azumi Shin yana karya azumi? Eh, shan ORS yana karya azumi saboda yana da ruwa da sinadarai masu gina jiki da ke shiga jiki don ciyarwa da ƙarfafa mutum. Duk abinda yake da gina jiki ko sinadaran da ke shigar da ruwa cikin jiki yana karya azumi. Shin ana…
Read More

Gwamnatin Tarayya na ƙoƙarin samar da ci-gaban tattali mai ɗorewa a Filato, inji Shettima

Daga BELLO A. BABAJI Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya jaddada aniyar Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da zaman lafiya da ci-gaban tattalin arziƙi mai ɗorewa a Jihar Filato da ma Nijeriya baki ɗaya. A lokacin da ya ke magana yayin ziyarar ta'aziyyar rasuwar Sheikh Sa'id Alhassan Jingir a gidan Shugaban Majalisar Malamai na Ƙungiyar Izala (JIBWIS) ɓangaren Jos, Sheikh Sani Yahaya Jingir, Shettima ya bayyana ƙoƙarin gwamnatin na ƙarfafa haɗin kan ƙasa da ci-gaba. Ya ce, Shugaba Bola Tinubu ya umarce shi da ya isar da gaisuwar ta'aziyyarsa gami da tabbatar wa mutanen Filato cewa gwamnatinsa ta fifita samun zaman…
Read More

‘Yar shekara 16 mai juna-biyu ta rataye kanta a Gombe

Daga BELLO A BABAJI Rundunar ƴan sandan Jihar Gombe ta tabbatar mutuwar wata ƴar shekara 16 mai suna Maryam Samuel, wadda ta kashe kanta a garin Kaltungo dake Ƙaramar Hukumar Kaltungo a jihar. Kakakinta, DSP Buhari Abdullahi ya bayyana hakan a ranar Asabar, inda ya ce yarinyar ta aikata hakan ne ta hanyar rataye kan nata a wata bishiya. Ya ce, lamarin ya auku ne a ranar 14 ga watan Maris, sa'o'i 24 bayan fitarta daga gida domin ɗebo itace a yankin gundumar Kalarin a ƙaramar hukumar, inda aka gano gawar yarinyar a rataye a wata bishiya dake kan dutsen…
Read More

Rikicin Sarauta: Gwamnatin Kano ta yi kira ga al’umma su kiyaye doka da guje wa tsoma baki a shari’a

Daga BELLO A. BABAJI Gwamnatin Jihar Kano ta yi kira ga al'umma da su kwantar da hankula da ƙaurace wa fusata juna tare da yin biyayya ga umarnin doka. A wani taron manema labarai na haɗaka tsakanin Ma'aikatun Shari'a da na Labarai na jihar ne aka bayyana hakan a yayin warware matsalolin hukuncin Kotun Ɗaukaka ƙara akan rikicin Masarautar Kano. Manyan jami'an gwamnati a taron sun ce, akwai buƙatar a bayyana wa al'umma haƙiƙanin matsayar kotu domin kauce wa ruɗar da su da labaran da ke tada hankulansu. A ranar 10 ga Junairu ne Kotun Ɗaukaka ƙara ta yi hukuncin…
Read More

‘Yan bindigar da suka yi garkuwa da gwarzon musabaƙa na neman miliyan N30

Daga BELLO A. BABAJI Gwamnatin Jihar Katsina ta ce, mahaddacin Al-ƙur'ani, Abdussalam Rabi'u Faskari da mahaifinsa da ɗan uwansa suna raye, amma a hannun ƴan bindigar da suka yi garkuwa da su. Kwamishinan Labarai da Al'adu na jihar, Dakta Bala Salisu Zango ya bayyana hakan a wata takarda da ya fitar a ranar Asabar. Kwanaki biyu da suka gabata ne aka yi garkuwa da su akan hanyarsu ta zuwa Faskari daga cikin garin Katsina bayan amsar gayyatar Gwamna Dikko Raɗɗa na ƙoƙarin da mahaddacin yayi a yayin musabaƙar da ta gabata. Kwamishinan ya ce, mahaddacin zai wakilci Nijeriya ne a…
Read More