19
Mar
Daga BELLO A. BABAJI Ƙungiyar Lauyoyin Nijeriya, NBA, ta yi tsokaci game da hukuncin da Shugaba Bola Tinubu ya yi na sanya dokar ta-ɓaci da dakatar da gwamna da zaɓaɓɓun ƴan majalisar dokoki a Jihar Ribas. Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne a yayin jawabinsa na ranar 18 ga watan Maris, inda ya ce ya yi hakan ne don kawo ƙarshen rikicin siyasar jihar. Saidai, a wata takarda da ke ɗauke da sanya hannun Shugabanta, Mazi Afam Osigwe (SAN), NBA ta ce hakan ya yi nesa da biyayya ga doka da tasiri ga tafiyar da harkokin demokraɗiyya musamman idan an…
