Babaji

5704 Posts

Goron Juma’a: Matakan kiyaye warin baki ga mai azumi

Daga CHIROMA AMINU ASID Yana da kyau a bi waɗannan matakai domin samun sauƙin matsalar, kuma kamar yadda na faɗa maku cewa, ba iya rashin yin brush bane ya ke kawo warin baki ga mai azumi. Yana da kyau a kiyaye da abubuwa kamar haka: 1.GOGE HAƘORA DA HARSHE DA KYAU– A tabbata an goge haƙora da makilin mai dauke da sinadarin fluoride bayan an sha ruwa dabayan sahur don kawar da ragowar abinci da ƙwayoyin cuta da suka maƙale a baki da saman harshe. 2.AMFANI DA ASWAKI – Yin aswaki yana taimakawa wajen kashe ƙwayoyin cuta kuma yana inganta…
Read More

Tambuwal, Dickson da Abaribe sun fice yayin da Majalisar Dattawa ta goyi bayan Tinubu kan sanya dokar ta-ɓaci a Ribas

Daga BELLO A. BABAJI A ranar Laraba ne Majalisar Dattawa ta amince da sanya dokar ta-ɓaci da Shugaba Bola Tinubu ya yi a Jihar Ribas. Saidai, a yayin zaman tattauna hakan ne Sanata Aminu Waziri Tambuwal da takwarorinsa - Sanata Seriake Dickson da Enyinnaya Abaribe suka fice cikin nuna rashin gamsuwa da matakin. Haka kuma, a yayin zaman na sirri ne aka ga sanatoci ukun suna nuna kiyayyarsu ga sanya dokar da dakatar da wasu zaɓaɓɓun ƴan siyasa a jihar, inda suka bayyana hakan a matsayin saɓa wa dokar ƙasa. Amma duk da boren nasu, majalisar sai da ta tabbatar…
Read More

Zuba jarin Dala biliyan 14 daga Indiya da wasu ƙasashe sun taimaka ga samar wa ƴan Nijeriya sauƙi – Gwamnatin Tarayya

Daga BELLO A. BABAJI Gwamnatin Tarayya ta ce, gwamantin Shugaba Bola Tinubu ta samar wa al'ummar Nijeriya sauƙi a harkokinsu na yau da kullum. Gwamnatin ta kuma yi sanadin zuba jarin da adadinsa ya kai Dala biliyan 14 daga ƙasar Indiya a ɓangarori da dama da cinikin Dala biliyan 8 na Indorama da kuma zuba jarin Dala biliyan 3.5 a tashar ƙarafuna a Jihar Akwa-Ibom. An bayyana hakan ne a yayin taron manema labarai na ma'aikatu da ya haɗa da Ministocin harkokin cikin gida da na waje, Olubunmi Tunji-Ojo da Yusuf Tuggar a Abuja. Ministan Cikin gida, Tunji-Ojo, ya ce…
Read More

Ba mu umarci a sako Nnamdi Kanu ba – NJC

Daga BELLO A. BABAJI Majalisar Alƙalan Nijeriya (NJC), ta musanta batun da ke yawo na cewa Alƙalin Alƙalai, Mai Shari'a Kudirat Kekere-Ekun ta umarci a gaggauta sako Shugaban ƙungiyar fafutukar kafa ƙasar Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu da aka tsare da mayar da shi ƙasar Kenya. Mataimakin Daraktan yaɗa labarai na NJC, Kemi Ogedengbe ya faɗa wa manema labarai hakan a Abuja. A ranar Juma'a ne za a sake gurfanar da Kanu a gaban Babbar Kotun Tarayya, inda Alƙali James Omotosho zai cigaba da sauraron ƙarar, bayan da Alƙali Binta Nyako ta tsame hannunta daga ciki saboda Kanu ya zarge ta…
Read More

Benue: ‘Yan sanda sun kashe ƴan bindiga da ƙwato makamai

Daga BELLO A. BABAJI Jami'an Rundunar ƴan sanda a Jihar Benue, sun yi nasarar kashe wasu ƴan bindiga da ƙwato makamai a yayin atisaye daban-daban. Sufeton ƴan sanda, Kayode Egbetokun ya yi alhinin rasuwar ɗaya daga cikin jami'an, wanda rasa ransa a yayin daƙile ayyukan ƴan bindigar. Jami'in hulɗa da jama'a na ƴan sanda, ACP Olumuyiwa Adejobi a wata takarda da ya fitar a ranar Alhamis, ya ce an gudanar da atisayen ne a ƙarƙashin umarnin Sufeton ƴan sandan. Ya ce, an yi hakan ne a ƙoƙarin jami'an na ganin an daƙile ayyukan garkuwa da mutane da fashi da wasu…
Read More

‘Yan bindiga sun kashe Shugaban Miyetti-Allah a Filato

Daga BELLO A. BABAJI A yammacin ranar Laraba ne wasu ƴan bindiga suka kashe Muhammad Adamu, wanda shi ne shugaban Miyetti-Allah - ƙungiyar Fulani Makiyaya (MACBAN), a Ƙaramar Hukumar Barikin Ladi dake Jihar Filato. Shugaban MACBAN na jihar, Ibrahim Yusuf Babayo ya bayyana hakan ga manema labarai a Jos, inda ya ce ƴan bindigar sun kai hari ne wa mamacin a gidansa, jim-kaɗan bayan shan ruwa. Ya ce, sun harbe shi ne sau adadi mai yawa, wanda daga bisani aka tabbatar da mutuwarsa a wajen da abin ya faru. Ya kuma yi alla-wadai da aukuwar lamarin tare da kira ga…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Atiku ya sanar da haɗakar jam’iyyun adawa a shirin zaɓen 2027

Daga BELLO A. BABAJI Ɗan takarar Shugaban ƙasa a zaɓen 2023 na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya sanar da haɗa ƙungiyar haɗakar jam'iyyun adawa don neman galaba akan Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027. Atiku ya bayyana hakan ne a taron manema labarai a Abuja, ranar Alhamis. Sauran jagororin da suka halarci taron sun haɗa da ɗan takarar Shugaban ƙasa a jami'yyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, wanda Yunusa Tanko ya wakilce shi; tsohon Sakataren Gwamantin Tarayya, Babachir Lawal; tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai; Sakataren ƙungiyar haɗakar jam'iyyun siyasa, Peter Ahmeh da Segun Showunmi da sauran su.…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Majalisar Wakilai ta amince da dokar ta-ɓaci a Ribas

Daga BELLO A. BABAJI Duk da cewa an samu wasu da suka nuna rashin goyon bayansu ga hukuncin, Majalisar Wakilai ta amince da sanya dokar ta-ɓaci a Jihar Ribas da Shugaba Bola Tinubu ya yi. A ranar Talata ne Shugaban ƙasar ya sanar da sanya dokar, biyo bayan ƙamari da rikicin siyasar jihar ya yi, inda ya dakatar da gwamnan jihar da mataimakiyarsa da kuma ɗaukacin mambobin Majalisar Dokoki ta jihar. Kakakin Majalisar, Tajuddeen Abbas ya bayyana cewa duk da cewa wasu na ganin batun bai samu adadin mutanen da ake buƙata ba, ya ce mambobi 243 ne suka halarci…
Read More

Kebbi: Mutanen da sanƙarau ta halaka sun kai 56

Daga BELLO A. BABAJI Ɓarkewar cutar sanƙarau, wadda a turance ake kira da 'cerebrospinal meningitis', ta yi sanadin mutuwar kimanin mutane 56 a ƙananan hukumomi uku dake Jihar Kebbi. Kwamishinan Lafiya na jihar, Alhaji Yunusa Musa Isma'ila, wanda Babban Sakataren Ma'aikatar, Dakta Shehu Nuhu Koko ya wakilce shi, ya tabbatar da hakan yayin ganawa da manema labarai a Birnin Kebbi, ranar Laraba. A yayin ganawar, an samu wakilci daga Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da Asusun Tallafa wa Yara ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) da kuma 'Medecins Sans Frontieres' (MSF). Kwamishinan ya ce, sun samu rahoto daga ofishin kula da…
Read More

Tarihin dokar ta-ɓaci a Nijeriya

Daga BELLO A. BABAJI Dokar ta-ɓaci a Nijeriya ba haye ba ce - gado ce ta iyaye da kakkani, inda wasu ke ganin an fara amfani da ita ne tun a siyasar Nijeriya ta farko a shekarar 1962 lokacin da aka yi zargin an samu manyan kura-kurai a ƙidayar jama'a ta farko da aka fara yi a ƙasar har ta kai ga aukuwar shahararren rikicin nan na kungiyar Action Group (AG) mai tasiri a yammacin Nijeriya. A ranar 1 ga watan Oktoba, firaministan ƙasar, Sir Abubakar Tafawa-Ɓalewa a wani jawabi da ya yi wa al'ummar ƙasar, ya shaida musu cewa…
Read More