Babaji

5704 Posts

Dokar ta-ɓaci a Jihar Ribas zubar da martabar Nijeriya ne – Jonathan ga Tinubu

Daga BELLO A. BABAJI Tsohon Shugaban ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan, ya ce dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara na Jihar Ribas da wasu zaɓaɓɓu zubar da martabar Nijeriya ne a idon duniya. Jonathan, a yayin taron Gidauniyar 'Haske Satumari Foundation Colloquium' a Abuja, ya koka kan yadda aka cire zaɓaɓɓun jami'an daga jagorancin jihar, wanda hakan zai sa a riƙa yi wa ƙasar mummunar kallo. Kalaman tsohon shugaban ƙasar sun biyo bayan sanya dokar ta-ɓaci ne da Shugaba Bola Tinubu ya yi a jihar, da dakatar da gwmanan da mataimakiyarsa gami da ƴaƴan Majalisar Dokokinta na tsawon watanni shida. Shugaba Tinubu…
Read More

Rufe VOA da Trump ya yi ya sanya Nijeriya da ƙasashen Afirka a tsaka-mai-wuya

Daga BELLO A. BABAJI Sanarwar dakatar da ayyukan gidan yaɗa labarai na VOA na Amurka da Shugaba Donald Trump ya yi, ya jefa Nijeriya da sauran ƙasashen Afrika shiga mawuyacin hali ganin yadda suka dogara da shi wajen samun labarai masu inganci da nuna ƙwarewa a yayin ayyukansa. VOA, ɗaya ne daga cikin gidajen rediyon ƙasa-da-ƙasa da ke aiki bisa gaskiya da adalci ba tare da ɗaukar ɓangare ko nuna wariya ba, wanda hakan ya sanya al'ummar Afirka suka mayar da shi madogara wajen samun ingantattu kuma sahihan labarai. A yayin da a wasu wuraren da gidajen jaridu ke samun…
Read More

Gwamnoni sun magantu kan dakatar da gwamnan Ribas

Daga BELLO A. BABAJI Ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya (NGF), ta cigaba da kare matakinta na yin shuru game da abubuwan da ke faruwa a harkokin siyasa a matsayinta na wadda ba ta da ɓangare a ire-iren batutuwan. A wata takarda da ta fitar a ranar Asabar, NGF ta ce ɗaukar ɓangare a lamuran da suka shafi jam'iyyu ka iya sa kawunan mambobinta su rabu kasancewar su ƴaƴan mabanbanta jam'iyyu. Hakan ya biyo bayan hukuncin sanya dokar ta-ɓaci a Ribas da Shugaba Bola Tinubu ya yi gami da dakatar da gwamnan jihar da wasu zaɓaɓɓun ƴan siyasa na tsawon watanni shida. Takardar,…
Read More

Osimhen ya zama ɗan wasa na biyu mafi zura ƙwallaye a tarihin Super Eagles

Daga BELLO A. BABAJI Ɗan wasa Victor Osimhen ya zama ɗan wasa na biyu a tarihin Super Eagles wajen zura ƙwallaye mafi yawa, bayan da ya ci ƙwallaye biyu a wasan da Nijeriya ta yi da Rwanda na neman gurbin shiga gasar Kofin Duniya na shekarar 2026, ranar Juma'a. Napoli ita ce ƙungiyar da ɗan wasan ya ke, duk da a yanzu yana matsayin na aro a Galatasaray, wanda ya zura ƙwallon farko ne a minti na 11, yayin da ya zura ta biyu ana dab da tafiya hutun rabin lokaci. A yanzu Osimhen yana da ƙwallaye 25 a matsayinsa…
Read More

Ɗantata Salihu ya zama Sakataren Labarai na Gidauniyar Ilimin Matasa da Ci-gabansu

Daga BELLO A. BABAJI Gidauniyar Ilimin Matasa da Ci-gabansu, ta naɗa Mallam Ɗantata Salihu a matsayin Sakataren Yaɗa labaranta na Ƙasa. Hakan ya biyo bayan kammala zama da masu-ruwa-da-tsaki na gidauniyar suka gudanar a Abuja ƙarƙashin jagorancin shugabanta, Hon. Kyari Jidai Gadzama, ranar Juma'a. Za kuma a rantsar da shi tare da sauran mambobin majalisar zartarwar gidauniyar a ranar da aka tsayar. Naɗin Salihu Ɗantata, wanda shi ne sakataren yaɗa labarai na farko a gidauniyar, an gabatar da shi ne na tsawon wa'adin shekaru biyar. Manufofin Gidauniyar sune tallafa wa matasa masu burin yin karatu a ɓangarori daban-daban da samar…
Read More

Kada ka yi gaggawar shiga wata maja – Tsohon shugaban ANP ga Kwankwaso

Daga BELLO A. BABAJI Jigo a Jami'yyar NNPP kuma tsohon shugaban tsohuwar Jam'iyyar ANP, Asiwaju Moshood Shittu, ya shawarci jagoran NNPP, Rabi'u Musa Kwankwaso kan cewa kada ya amsa duk wata gayyata ko tayin shiga wata jam'iyyar haɗaka ta ƴan adawa. Shittu ya bayyana hakan ne la'akari da abinda ya faru a shekarar 2014 na haɗa ƴan siyasa waje guda da nufin karɓe mulki a hannun tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan ba tare da zaɓo ƙwaƙƙwaran ɗan takara ba. Ya ce, lallai akwai buƙatar Kwankwaso ya yi nazari game da wanda za a tsayar takara da manufar yin majar.…
Read More

Babban jigo a NNPP ya yaba wa Kwankwaso bisa kalamansa kan sanya dokar ta-ɓaci a Ribas

Daga BELLO A. BABAJI Tsohon Shugaban tsohuwar Jam'iyyar ANP kuma Darakta-Janar na majalisar yaƙin neman zaɓen Rabi'u Musa Kwankwaso a Arewa, Asiwaju Moshood Shittu, ya jinjina wa Kwankwaso bisa nuna dattako akan matsalar sanya dokar ta-ɓaci a Ribas, wanda Majalisar Dokoki a mataki na ƙasa ta amince da shi. Ya ce, matakin da ɗaya daga cikin manyan ƙasar ya ɗauka ya nuna yadda ya ke da sanin ya kamata da kishi gami da ƙwarewa. Ya kuma ce, Kwankwaso mutum ne wanda ba ya gaggawar tsoma baki akan wani abu don gamsar da mutane, saidai ya na la'akari ne da abinda…
Read More

Gwmanan Kano ya umarci muƙarrabansa su bayyana kadarorinsu

Daga BELLO A. BABAJI Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya umarci baki ɗaya jami'an gwamnatinsa da ya naɗa a muƙamai daban-daban da su bayyana kadarorin da suka mallaka. Gwmanan ya bayyana hakan ne a yayin buɗe-baki da jagororin ma'aikata da masu ba shi shawara na musamman a Gidan Gwamnatin jihar. Ya ce, kaso 60 zuwa 70 na muƙarraban nasa ba su kiyaye abinda doka ta shar'anta masu ba, ya na mai kira a gare su da su bai wa doka haɗin kai wajen gaggauta bada duk wata takarda da aka buƙaci su kawo. Haka kuma ya shawarci mashawartansa da…
Read More

MOPPAN ta jinjina wa gwamnan Kano bisa ɗaukar nauyin rashin lafiyar tsohuwar jaruma, Halisa Muhammad

Daga BELLO A. BABAJI Ƙungiyar ƴan fim ta Ƙasa, MOPPAN, ta yaba wa Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano bisa ƙoƙarinsa na ɗaukar ɗawainiyar rashin lafiyar Hajiya Halisa Muhammad. Halisa Muhammad, mamba ce ta masana'antar finafinan Kannywood kuma tsohuwar jaruma, wadda ke fama da cutar daji. Shugaban MOPPAN, Malam Mai-Kuɗi ya bayyana hakan a wata takarda da Kakakin ƙungiyar, Ibrahim Amarawa ya fitar, inda ya ce hakan ya nuna yadda gwamnan ya damu da mutanensa da ma mambobin Kannywood. Ya kuma ce za su cigaba da bai wa Gwamantin Kano cikakken goyon baya ga ayyukanta da kuma ƙoƙarin kawo…
Read More

Kotun Ƙoli ta tabbatar da na hannun daman Wike a matsayin halastaccen Sakataren PDP na Ƙasa

Daga BELLO A. BABAJI Kotun Ƙoli ta tabbatar da Samuel Anyanwu, wanda na hannun dama ne ga Ministan Abuja, Nyesom Wike, a matsayin halastaccen Sakataren jami'yyar PDP na Ƙasa. A wani hukunci na tawagar alƙalai biyar, kotun ta ce lamuran da suka shafi shugabanci ko zama mamba, abubuwa ne na cikin gida ba waɗanda kotu za ta tsoma baki aciki ba. Da haka ne kotun ta ture hukuncin Babbar Kotun Tarayya ta Jihar Enugu, wanda aka yi a ranar 20 ga watan Disambar 2024 na tabbatar da cire Anyanwu daga muƙamin, inda ta ce kotun ba ta da hurumin yin…
Read More