Babaji

5704 Posts

A karon farko gwamnan Ribas ya shigo cikin jama’a tun bayan dakatar da shi

Daga BELLO A. BABAJI A ranar Lahadi ne aka ga Gwamna Siminalayi Fubara da aka dakatar cikin jama'a tun bayan sanya dokar ta-ɓaci a Jihar Ribas. Fubara, wanda aka dakatar na tsawon watanni shida a ranar Talata, an gan shi ne sanye da farin kaya. Hakan ya biyo bayan fitowarsa ne zuwa coci domin yin addu'o'i na addininsa na Kiristanci da aka saba yi, inda ya halarta tare da wasu makusantansa. A ranar Talata ne Shugaba Bola Tinubu ya sanar da sanya dokar ta-ɓaci a jihar bayan samuwar rikicin siyasa da ka iya haifar da tsaiko ga zaman lafiyar al'umma,…
Read More

X: NFF ta sanar da shafin bogi da aka buɗe da sunan kocin Super Eagles, Eric Chelles

Daga BELLO A. BABAJI Hukumar Ƙwallon ƙafa ta Ƙasa, NFF, ta ankarar da al'umma game da shafin bogi da aka buɗe a kafar X da sunan kocin Super Eagles, Éric Chelle. A sanarwar da fitar ta kafar, NFF ta ce Chelle bai da wani shafi a kafar, inda ta yi gargaɗin cewa kada a jingina masa abinda aka gani a can, wanda ƴan damfara ne suka buɗe shi. Ta ce shafinsa guda ɗaya ne, wanda shi ne a [@eric_chelle] a kafar Instagram. Don haka ta yi kira ga al'umma da su riƙa amfani da shi wajen ɗaukar labaran da suka…
Read More

Za a sallamo Pafaroma daga asibiti bayan shafe makonni

Daga BELLO A. BABAJI Pafaroma zai koma Fadar Vatican inda zai shafe aƙalla watanni biyu kafin ya murmure, kamar yadda ɗaya daga cikin likitocinsa ya bayyana. An kwantar da Pafaroma mai shekaru 88 ne a Asibitin Gemelli dake Birnin Rome a ranar 14 ga watan Fabrairu. Lamarin da ya auku sakamakon rashin lafiyar da ta shafi numfashi wadda ta sauya zuwa nimoniya. Hakan ya biyo bayan sanarwar da Vatican ta yi ne a makon da ya gabata na cewa jagoran ya na samun sauƙi daga halin da ya shiga.
Read More

An yi garkuwa da wata soja da mutane biyu a Abuja

Daga BELLO A. BABAJI A ranar Juma'a ne wasu ƴan bindiga suka yi garkuwa da wata sojar ruwa da ke aiki a Hedikwatar Tsaro a Abuja, wadda ba a bayyana sunanta ba. An yi garkuwa da ita ne tare da wasu mutane biyu a gidajensu dake unguwar Mpape, kamar yadda wata majiya daga sojoji ta bayyana. Majiyar ta kuma ce, ƴan bindigar sun buƙaci a biya su miliyan N100 a matsayin kuɗin fansa kafin a sako su. Zuwa lokacin haɗa rahoton, ba a samu jami'an yaɗa labarai na hedikwatar a waya ba domin ji bakunansu, kuma ba su amsa saƙon…
Read More

‘Yan bindiga sun farmaki masallata da kashe mutane 44 a Nijar

Daga BELLO A. BABAJI Lamarin ya auku ne a ranar Juma'a yayin da masallatan suke tsaka da sallar juma'a a ƙauyen Fombita na yankin Kokorou, wanda kusa ya ke da iyakar ƙasashe Nijar, Burkina Faso da Mali, kuma cibiyar masu ikirarin jihadi a Yammacin Afrika da ke alaƙanta kansu da Al-ƙa'ida. Ma'aikatar Tsaro ta Nijar ta ɗora alhakin harin akan ƙungiyar EIGS da ake jingina ta ga ƙasar musulunci, kamar yadda ta bayyana a wata sanarwa, ranar Juma'a. Bayan harin masallatan ne sai maharan kuma suka cinna wuta a wata kasuwa da wasu gidaje a yankin. Sanarwar ta ƙara da…
Read More

Kotu da ta bada damar yi wa Sanata Natasha kiranye

Daga BELLO A. BABAJI Babbar Kotun Tarayya dake Lokoja a Jihar Kogi, ta yi hukuncin haramta wa Hukumar Zaɓe (INEC) karɓar yin kiranye da al'ummar mazaɓar jihar ta Tsakiya suka yi akan Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan. Kotun, wadda ta yi hukuncin a ranar Juma'a, ta tabbatar da cewa yin kiranyen abu ne da doka ta amince da shi kuma al'umma suna da damar su yi hakan. Ta kuma yi kira ga al'ummar mazaɓar da su gudanar da abinda doka ta sahale masu cikin kwanciyar hankali da lumana. Lamarin ya biyo bayan hukuncin Kotun ne na hana INEC da jami'anta karɓa ko…
Read More

WASSCE ta 2025: WAEC ta fitar da sakamakon jarrabawar komfuta na ɗaliban makarantu masu zaman kansu

Daga BELLO A. BABAJI A ranar Asabar ne Hukumar gudanar da jarrabawar makarantun sakandare ta yammacin Afirka, wato WAEC, ta sanar da fitar da sakamakon jarrabawar rukunin farko na ɗaliban babbar sakandare da suka yi a komfuta ta shekarar 2025. Hukumar ta wallafa hakan ne a shafinta na X, inda ta ce na ɗaliban makarantu masu zaman kansu ne aka fitar. Ana gudanar da jarrabawar ne da ake kira da Computer-base a makarantun gwamnati da masu zaman kansu domin zamanantar da tsarin jarrabawa ga ɗaliban wanda ake yi a kowace shekara.
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: ‘Yan sanda da sojoji sun ceto jami’in sojan ruwa da wasu da aka yi garkuwa da su

Daga BELLO A. BABAJI Rundunar ƴan sanda da haɗin-gwiwar sojoji a Abuja, sun yi nasarar ceto wani jami'in sojan ruwa da wasu mutum biyu da aka yi garkuwa da su a yankin Mpape, ranar Juma'a. Kakakin rundunar, SP Josephine Adeh ta bayyana hakan a ranar Lahadi cikin wata takarda, inda ta ce a daren ranar ne aka samu wasu ƴan bindiga a yankin rukunin gidajen Maman Vasta da suka buɗe wa al'umma wuta tare da yin garkuwa da mutane ukun. Jim-kaɗan bayan haka ne ƴan bindigar suka kira makusantan sojan, inda suka nemi a biya su Naira miliyan 500 a…
Read More

Waiwaye: Yadda Fayose ya gargaɗi Fubara akan rigima da Wike tun a 2023

Daga BELLO A. BABAJI Tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya gargaɗi Gwamnan Ribas da aka dakatar, Siminalayi Fubara kan yin rigima da magabacinsa na jagorancin jihar, Nyesom Wike. A lokacin da ya ke magana a watan Mayu na 2023 a taron karrama Wike bayan ya miƙa mulki ga Fubara, Fayose ya bayyana cewa, Wike mutum ne da ba ya karɓar faɗuwa yayin da ake faɗa da shi. Ya shawarci Fubara da cewa ya gudanar da harkokinsa cikin kulawa da ƙaurace wa abinda ya fi ƙarfinsa. Fayose ya tabbatar da cewa ya san Wike a matsayin wanda idan ya ce…
Read More

An kama soja da ɗan sanda bisa satar batiran jirgin ƙasa a Kaduna

Daga BELLO A. BABAJI An kama wani jami'in soja da wani ɗan sanda mai suna Ajiye Joel bisa laifin sace wasu batira daga Hukumar Jiragen ƙasa ta Ƙasa (NRC) tare da wani jami'in hukumar a Jihar Kaduna. Sahara Reporters ta ruwaito cewa, wani jawabin ƴan sanda ya nuna cewa dakarun sojojin atisayen 'Fansan Yamma' ne suka kama mutane ukun a ranar 19 ga watan Maris. Dakarun haɗaka na atisayen, an ware su ne musamman don daƙile ayyukan ta'addanci a yankin Arewa maso Yammacin Nijeriya. Tuni dai aka tsare su a reshe na ɗaya na jami'an sojoji dake Kaduna yayin da…
Read More