26
Mar
Daga BELLO A. BABAJI An samu tsaiko game da ƙorafin kiranyen Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta Kogi ta Tsakiya da aka shigar wa Hukumar Zaɓe (INEC), bayan da hukumar ta ce akwai wasu sharuɗɗa da ƙorafin ya gaza cikawa. Kwamishinan hukumar na ƙasa kuma Shugaban Labarai da Ilimantar da Masu zaɓe, Sam Olumekun ya bayyana hakan a wata takarda, ranar Alhamis. Ya ce, za su yi aiki ne da ƙorafin a ƙarƙashin dokar ƙasa, wadda ta bada damar hakan, saboda haka sai an cika ƙa'idodin da ta gindaya kafin hukumar ta yi aiki a kai. Olumekun ya ce, sun karɓi kundin…
