Babaji

5704 Posts

Gwamna Mutfwang ya yi buɗe-bakin Ramadan da Musulmi a Jos

Daga HABU ƊAN SARKI Jos Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang ya yaba wa gudunmawar da al'ummar Musulmi suke bayarwa ga cigaban zaman lafiya da tsaro a jihar tare da jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci duk wani mai son tayar da fitina ya samu nasara ba. Ya ce, daga yanzu babu wani yanki na Jos da za a ce mallakar Musulmi ne ko na Kirista, har kuma ana barazana ga rayuwar wani ko wasu a yankin. "Jihar Filato ta kowa ce, kuma babu wani yanki da za a ce wani ba shi da ƴancin shiga ko zama. Ba za…
Read More

Mun haramta Hawan Sallah a Kano bisa shawarar gwamnatin jihar – ‘Yan sanda

Daga BELLO A. BABAJI Rundunar ƴan sandan Jihar Kano ta sanar da hana gudanar da Bikin Hawan Sallah a yayin Sallah Ƙarama ta 2025 sakamakon waɗansu dalilai na tsaro, don cigaba da wanzar da zama lafiyar al'umma. Kwamishinan rundunar, CP Ibrahim Adamu Bakori ya bayyana hakan a yayin ganawa da manema labarai a hedikwatar hukumar dake Bompai a jihar, ranar Juma'a. Bakori ya ce, lallai akwai buƙatar su kula da zaman lafiyar al'umma a yayin gudanar da bukukuwa. Ya bayyana cewa, akwai barazanar tsaro a jihar wanda hakan ka iya haifar da asarar rayuka da dukiyoyin al'umma, lamarin da bayanan…
Read More

Sarkin Musulmi ya umarci a duba jinjirin watan Ƙaramar Sallah

Daga BELLO A. BABAJI Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Ƙoli kan Harkokin Addini, Muhammad Sa'ad Abubakar na III, ya yi kira ga ɗaukacin al'ummar Musulmi a Nijeriya da su fara duba watan Ƙaramar Sallah, wato Shawwal daga ranar Asabar, 29 ga watan Maris. A wata takarda da ke ɗauke da sanya hannun Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaidu, wanda kuma shi ne Shugaban kwamitin mashawarta na harkokin addini a majalisar Sarkin, ya ce ganin watan zai bada damar sauke azumi da kuma gudanar da shungulan Sallar ta Eid el-fitr. Ya kuma yi kira ga al'umma su ruwaito duk wani sahihin…
Read More

Sojoji sun kashe jagoran ƴan bindiga, Ɗan Isihu a Zamfara

Daga BELLO A. BABAJI A ƙoƙarinsu na daƙile ayyukan ta'addanci a yankin Arewa maso Yammacin Nijeriya, dakarun tsaro na Operation 'FANSAN YAMMA', sun yi nasarar kashe shahararren jagoran ƴan bindiga, Ɗan Isihu a wani atisayen sirri da sojoji suka gudanar. A ƴan shekarun nan ne ɗan bindigar ya adabi yankuna da dama a Jihohin Zamfara, Katsina da Kaduna, inda ya shahara da garkuwa da mutane da kai hare-hare gami da tarwatsa garuruwa, lamarin da ya yi sanadiyyar rasa rayukan al'umma da ɗaiɗaita wasu da dama. Haka kuma, Ɗan ta'addar ya kasance mai tilasta wa ƙauyuka biyan haraji, gudanar da muggan…
Read More

Za a yi addu’o’i na musamman yayin cikar shekaru 73 na Shugaba Tinubu a Babban Masallacin Ƙasa na Abuja

Daga BELLO A. BABAJI A ranar 29 ga watan Maris ne za a yi addu'o'i na musamman a babban Masallacin Ƙasa na Abuja, a yayin da Mai Girma Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke cika shekaru 73 a duniya. Kakakinsa, Bayo Onanuga ya bayyana hakan a ranar Alhamis cikin wata takarda, inda ya ce Shugaban zai kuma yi amfani da damar hakan wajen gode wa Allah SWT da Ya yi riƙo da hannunsa wajen jagorancin al'ummar Nijeriya. Lamarin da ya dace da watan Ramadana kuma watanni biyu gabannin cikarsa shekaru biyu akan karagar mulki. Za kuma a yi addu'o'i ga ƙasa…
Read More

Gwamnan Filato ya yi jimamin rasuwar fitaccen jarumi, Karƙuzu

Daga BELLO A. BABAJI Gwamnan Jihar Filato, Barista Caleb Mutfwang, ya bayyana alhininsa game da rashin fitaccen jarumin finafinan Hausa, Abdu Kano da aka fi sani da Karƙuzu, wanda ya rasu bayan fama da wani rashin lafiya. A saƙon ta'aziyyarsa da ke ɗauke da sanya hannun Daraktan yaɗa Labaransa, Gyang Bere, gwmanan ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai hikima wanda mutuwarsa ta haifar da babban giɓi ga iyalansa da masana'antar finafinai da jihar da ma ƙasa baki ɗaya. Ya ce, Karƙuzu ya bada gagarumar gudummawa a harkokin finafinan Hausa ta hanyar amfani da shirye-shiryensa wajen ilmantar da al'umma, nishaɗantar…
Read More

Idon al’umma a kanku ya ke, ku riƙa adalci koyaushe – Shettima ga alƙalai

Daga BELLO A. BABAJI Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya yi kira ga alƙalai da su ƙaurace wa ababen zargi tare da tabbatar da gaskiya da adalci a yayin ayyukansu, ranar Laraba. Shettima ya bayyana haka ne a yayin lakcar buɗe zauren alƙalai na BoB a Abuja, inda ya ce al'umma na da maƙuran tunanin samun adalci daga gare su duk da cewa a wasu lokutan akan samu jinkirin yanke hukunci akan shari'o'i a sakamakon wasu uzururruka. Ya ce, dokoki ababe ne da sai da su al'umma za ta zauna lafiya a yayin zamantakewa, don haka lallai sai an samu…
Read More

Yadda Majalisar Ɗinkin Duniya ta karrama masu gajerun finafinai don SDGs

Daga BELLO A. BABAJI A ranar Laraba, 26 ga watan Maris, 2025 ne aka gudanar da taron ƙaddamar da bugu na uku na fim ɗin raya manufofin shirin samar da ayyukan ci-gaba masu ɗorewa (SDG's) a Nijeriya da kuma karrama jaruman da suka yi aikin fitar da shi. Taron, wanda aka gudanar da a ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya (MƊD) na Nijeriya da ke Abuja, ya samu wakilci daga Fadar Shugaban ƙasa, jaruman finafinan Nollywood, Ministan Ma'aikatar Masana'antu masu Ƙirƙira, ƴan jaridu da sauran su. A lokacin da ya ke jawabi a taron, Kodinetan MƊD a Nijeriya, Mohamed Malick Fall ya…
Read More

Natasha: INEC ta sanar da fara aiki kan ƙorafin kiranye

Daga BELLO A. BABAJI Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, ta sanar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da aka dakatar batun ƙorafin kiranye da ƴan mazaɓarta suka shigar wa hukumar akanta. A wani saƙo da aka aika wa Natasha, da ke ɗauke da sanya hannun Sakatariyar INEC, Rose Oriaran Anthony, ta ce matakin karɓar ƙorafin da hukumar ta ɗauka, ya ta'allaƙa ne da sakin-layi na 69 na dokar ƙasa a kundin 1999. Haka ma sanar da ita batun, wanda sashe na 2 na dokokin hukumar na 2024 ne ya bada dama, sannan an wallafa batun a shafin yanar gizo na INEC. Saidai,…
Read More

Ƙungiyar KAFIGAN ta jajenta rasuwar fitaccen Jarumi Baba Karƙuzu

Daga BELLO A. BABAJI Ƙungiyar ƴan finafinan Kannywood, wato KAFIGAN, ta yi alhini tare da jajenta rasuwar tsohon ɗan wasan fim ɗin Hausa, Malam Abdullahi Shu'aibu da aka fi sani da Karƙuzu Na-Bodara. Karƙuzu ɗaya ne daga cikin taurarin finafinan Hausa da suka jima suna nishaɗantar da al'umma musamman a ƙasar Hausa, wanda mutuwarsa ta haifar da babban giɓi ga masana'antar, inda zai yi wahala a maye gurbin da ya bari. Darakta-Janar na KAFIGAN, Hon. Adamu Bello ya bayyana jimaminsa game da babban rashin tare da masa addu'ar fatan samun rahamar Allah (SWT). Ya kuma yi ta'aziyya ga iyalansa da…
Read More