30
Mar
Daga BELLO A. BABAJI Ƙungiyar Matasan Arewa ta AYCF, ta ƙaryata kalaman da Honorabul Aminu Sani Jaji ya yi, inda ta ce hakan wani yunƙuri ne na yin rufa-rufa ga harkokin siyasarsa mai cike da alamomin tambaya. Shugaban ƙungiyar, Alhaji Yerima Shettima ya ce, take-taken Jaji salo ne na cika burinsa a siyasa duk da cewa ya bar baya da ƙura domin akwai zarge-zargen almundahana da sauya aƙalar kuɗaɗe a harkokin jagorancinsa. Shettima ya hasato zamanin Buhari, a lokacin da Jaji ya jagoranci yi wa Buhari kamfen, inda ya ce daga baya ya koma amfani da damar hakan wajen azurta…
