Babaji

5704 Posts

Haramta gangami ba zai hana ni zuwa gida hutun sallah ba – Natasha ga Gwamnatin Kogi

Daga BELLO A. BABAJI A ranar Talata ne Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da ke wakiltar mazaɓar Kogi ta Tsakiya ta bayyana cewa, ba za ta janye batun zuwanta gida hutun Sallah ba. Ta yi kira ga magoya bayanta da su yi watsi da jita-jitar da ke yawo na cewa ta soke zuwa hutun Sallah. Ta bayyana hakan ne ta hannun tawagar watsa labaranta a wata sanarwa. Hakan na zuwa ne jim-kaɗan bayan Gwamantin jihar ta fitar sanarwar haramta yin gangami da wasu tarurruka bisa zargin barazanar tsaro. Haka kuma ta dakatar da yin ayyuka kamun kifi (su) da makamantansa sakamakon rasa…
Read More

Shari’ar Turaki da Hadiza: Ka binciki wacce ta yi zargin cin zarafi – Ɗantata ga Sufeto Janar

Daga BELLO A. BABAJI Ƙungiyar Masu Sharhi kan Harkokin Tsaro ƙarƙashin jagorancin Daraktan Tsaro a Shirin 'Security of the Salute of Nigeria Initiative', Kwamared Salihu Ɗantata Mahmud, ta yi kira ga Sufeton Janar na rundunar ƴan sanda, Kayode Egbetokun, da ya gudanar da bincike na sirri akan Hadiza Baffa, wacce ta zargi tsohon Ministan Ayyuka na Musamman, Tanimu Turaki (SAN) da cin zarafin. Ɗantata ya nemi a yi binciken ne don tabbatar da gaskiya ko akasin hakan game da kalaman nata akan Turaki. Ya ce, akwai da dama daga cikin waɗanda ta yi wa irin zargin da ke cikin kundin…
Read More

Kisan Edo: Gwmnan jihar ya ziyarci Kano, ya yi alwashin tabbatar da adalci akan waɗanda aka kashe

Daga BELLO A. BABAJI Gwamna Monday Okpebholo ya yi alla-wadai da kisan wulaƙancin da aka yi wa mafarauta 16 a yankin Udune dake Ƙaramar Hukumar Uromi a Jihar Edo, ya na mai cewa ba za su bari ya tafi a banza ba. Gwmanan ya faɗi hakan ne a yayin ziyarar ta'aziyya ga Gwamna Abba Kabir Yusuf da al'umma a Gidan Gwamnatin Jihar Kano, ranar Litinin. Okpebholo ya bayyana alhininsa a lokacin da ya haɗu da al'ummar Hausawa, waɗanda ya ce sun taimaka masa a lokacin yaƙin neman zaɓensa da ma lokacin da aka gudanar da zaɓen watanni kaɗan da suka…
Read More

‘Yan sanda sun kama ɗan shekara 20 bisa kisan dogarin Sarki Sanusi yayin Sallar Idi

Daga BELLO A. BABAJI Rundunar ƴan sanda a Jihar Kano, ta ce ta kama wani matashi ɗan shekara 20 bisa zargin sa da kashe dogarin Sarki Muhammadu Sanusi II a filin Idi. Lamarin, wanda ya faru a ranar Lahadi, ya yi sanadin mutuwar wani ɗan bijilante da kuma raunata wani ɗaya. Haka kuma akwai wani jami'in da ya samu rauni, wanda a yanzu ya na Asibitin Murtala a Kano, inda ya ke karɓar magani. A wata sanarwa da ta fitar ta hannun Kakakinta, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, rundunar ta ce, an kama wani mai suna Usam Sagiru da hannun a…
Read More

Rikicin sarauta: NGO ta yi tir da gwamnatin Kano kan ƙin bin doka da zaman lafiya

Daga BELLO A. BABAJI Wata ƙungiyar NGO a Kano da ke shirye-shiryen samar da jagoranci na gari, ta soki Gwamnatin jihar da Sarki Muhammadu Sanusi II bisa zargin su da ƙin yin biyayya ga hukuncin doka da kuma zaman lafiyar al'umma. A wata takarda da ta fitar a Kano, ranar Litinin, ƙungiyar ta ce da Gwamna Abba Kabir Yusuf da Sarkin duk sun yi buris da umarnin ƴan sanda na hana hawan sallah a Kano a yayin bukukuwan Sallah. Tun farko, rundunar ƴan sanda jihar ta fitar da sanarwar hana yin bikin hawan sallah da aka saba yi a kowace…
Read More

Ku jingine ƙudirin neman hukunta ƴan Nijeriyan da ba su yi zaɓe ba – SERAP ga Majalisar Dokoki

Daga BELLO A. BABAJI Ƙungiyar tabbatar da gaskiya da adalci kan zamantakewa (SERAP), ta yi kira ga Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio da Kakakin Majalisar Wakilai, Tajuddeen Abbas da su gaggauta janye ƙudirin neman tasa ƙeyar waɗanda ba su yi zaɓe ba a matakin jiha ko tarayya zuwa gidan yari na wata shida da kuma ko ƙaƙaba masu tarar N100,000. A ranar Asabar ne ƙungiyar ta kare haƙƙin ɗan-adam, a wata takarda daga Mataimakin Daraktanta, Kolawole Oluwadare ta bayyana hakan da cewa za ta ƙalubalanci ƙoƙarin tabbatar da ƙudirin a kotu matuƙar ba su janye shi ba. Ta ce, ƙoƙarin…
Read More

Mai ya sa ka ke ƙarya a Ramadan – Wike ga Atiku kan zaɓen 2023

Daga BELLO A. BABAJI Ana cigaba da faɗi-in-faɗa a tsakanin tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da Ministan Abuja Nyesom Wike game da zaɓar mataimakin na farkon a zaɓen 2023. Manyan ƴaƴan Jam'iyyar PDP'n sun samu rabuwa ne a lokacin da kowane ɗaya daga cikin su ya nemi zama ɗan takarar jam'iyyar a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2023, inda Atiku ya zo na ɗaya tare da zaɓar tsohon gwamnan Delta, Ifeanyi Okowa a matsayin mataimaki a gare shi madadin Wike da ya zo na biyu a zaɓen fidda gwani. A baya, Atiku ya ce ya zaɓi tsohon gwamnan na…
Read More

‘Yan Shi’a suka fara harbin sojoji, inji shugabannin tsaro

Daga BELLO A. BABAJI Rundunar Sojojin ƙasa ta ɗora musabbabin rikicin da ya faru a Abuja tsakanin masu zanga-zanga da jami'an tsaro akan masu zanga-zangar, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 12. A ranar Juma'a ne aka gudanar da zanga-zangar ƙarƙashin ƙungiyar Shi'a ta IMN da aka dakatar, waɗanda suka yi taron ranar Ƙudus da nufin shiga sahun masu gangamin goyon bayan Palastine. Wani rahoton sirri ya ce, 11 daga ƴan zanga-zangar da soja ɗaya ne suka rasa rayukansu a yayin karambattar. Ƙungiyar Amnesty International a Nijeriya ta ce sojojin sun yi harbe-harbe ne acikin ƴan zanga-zangar a yunƙurinsu na…
Read More

Kisan Edo: Gwamna ya dakatar da shugaban tsaro da haramta ayyukan bijilante a jihar

Daga BELLO A. BABAJI Gwmanan Jihar Edo, Monday Okpebholo ya umarci a dakatar da baki ɗaya haramtattun ƙungiyoyin ƴan bijilante da ke gudanar da harkokinsu a jihar. Ya kuma dakatar da kwamandan jami'an tsaro na jihar, CP Friday Ibadin (mai ritaya). A wata takarda da Sakataren gwamnatin jihar, Umar Musa Ikhilor ya fitar, gwamnan ya bayyana hakan ne biyo bayan iftila'in da ya faru a garin Uromi na Ƙaramar Hukumar Esan ta Arewa a jihar, inda aka kashe wasu matafiya ƴan Arewa guda 16 a ranar Alhamis. Ya ce, jami'an ƴan bijilante da suka jagoranci kisan matafiyan a ranar 27…
Read More