‘Yan sanda sun kama ɗan shekara 20 bisa kisan dogarin Sarki Sanusi yayin Sallar Idi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Rundunar ƴan sanda a Jihar Kano, ta ce ta kama wani matashi ɗan shekara 20 bisa zargin sa da kashe dogarin Sarki Muhammadu Sanusi II a filin Idi.

Lamarin, wanda ya faru a ranar Lahadi, ya yi sanadin mutuwar wani ɗan bijilante da kuma raunata wani ɗaya.

Haka kuma akwai wani jami’in da ya samu rauni, wanda a yanzu ya na Asibitin Murtala a Kano, inda ya ke karɓar magani.

A wata sanarwa da ta fitar ta hannun Kakakinta, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, rundunar ta ce, an kama wani mai suna Usam Sagiru da hannun a harin.

Haka kuma, ta ce an gayyaci Shamakin Kano, Alhaji Wada Isyaku don gudanar da bincike akan sa game da lamarin.

Sannan, rundunar ta jaddada batun haramta bikin hawan sallah a jihar, a ƙoƙarinta na tabbatar da wanzar da zaman lafiya acikin al’umma inda ta ce duk wanda aka samu da hannu aciki aikatawa, doka za ta yi aiki akansa.

Bugu da ƙari, ta yi gargaɗi ga masu ayyukan dabanci, inda ta ce lallai za ta sa ƙafar wando ɗaya da waɗanda aka kama suna iri aikin.

Ta kuma yi kira ga al’umma da su kasance masu bai wa jami’an tsaro haɗin kai don tabbatar da zaman lafiya a yankunansu.

By Babaji