Tinubu ne zai sake lashe zaɓen 2027 – Maituraka

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Jigo a jam’iyar APC na Jihar Katsina Alhaji Abdulaziz Maituraka ya ce in Allah ya yadda jam’iyar ne za ta sake lashe zaɓe mai zuwa a matakin jihar da ƙasa baki ɗaya.

Ya yabawa gwamntin Tinubu kan matakin da take ɗauka na karyo da farashin kayan abinci da kawo ƙarshen ta’adanci a wasu jihohi na Arewacin ƙasar.

Maituraka yayi kira da a gyara da gina sabbin hanyoyi a faɗin kasar da kuma gina al’umma na daga cikin aikace-aikacen da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya sa a gaba .

Ya ce waɗannan ma kaɗai sun isa a sake zaɓen gwamnatin APC daga sama har ƙasa.

Maituraka wanda kuma mataimaki na musamman ne a ofishin mataimakin shugaban Majalisar Dattijai Barau Jibrin ya jinjina wa Gwamna Dikko Raɗɗa kan yadda yake aiwatar da ayyukan ci gaban jihar.

Daga baya ya rabawa zaɓaɓɓun kansiloli da dattawan jam’iyar APC na wakilin kudu a Katsina goron sallah.

By ukarofi