Hon. Hamza Sule ya yi bikin sallah tare da al’ummarsa a Faskari

Spread the love

Jigon ɗan siyasa, ɗan kasuwa, kuma kwamishinan Muhalli na Jihar Katsina, Hon. Hamza Sule Faskari, ya yi bikin sallah tare da al’umarsa a garin Faskari inda ya amshi gaisuwar barka da Sallah daga ƙungoyin daban daban.

Hamza Sule wanda shine Wamban Faskari kuma Sadaukin ƙasar Hausa, ya amshi baƙuncin ƙungiyoyin ‘yan siyasa, da matasa, da marasa galihu, da ƙungiyoyin ci gaban al’umma a gidansa da ke Faskari, ya kuma sada zumunci da ‘yan uwa da abokan arziki.

Kamar yadda ya saba, Hon. Hamza Sule ya yi ma baƙin nasa liyafar cin abinci game da basu goron Sallah da jagorantar gudanar da addu’o’i ga jiha da ƙasa baki ɗaya.

Kowace mazaɓa a Ƙaramar hukumar Faskari ta samu Naira 500,000 yayin da mazaɓu uku suka samu ƙarin Naira 200,000 domin la’akari da yawan waɗanda suka kawo masa ziyara daga mazaɓun, inda jimillar kuɗin ya kai Naira 5,600,000.

Haka zalika ƙungiyoyin ‘yan siyasa guda biyar sun samu jimillar Naira 2,500,000 inda kowace ƙungiya ta samu Naira 500,000 domin ƙara musu ƙwarin gwiwa a ayyukan da suke yi.

Ƙungiyoyin sune Wambai Support Organisation Funtua Zone, Wambai Mataki na Gaba Funtua Zone, Wambai Political Awareness Funtua Zone, 11 Thousand for Wamban Faskari Funtua Zone, da Wambai House to House Funtua Zone.

Tawagar ƙungiyoyi daban-daban daga ƙaramar hukumar Sabuwa suma sun samu Naira miliyan uku yayin da wata ƙungiya daga ƙaramar hukumar Ɗandume ta samu Naira 500,000 a matsayin goron Sallah.

Hon. Hamza Sule ya kuma yi amfani da bikin Sallar wajen tallafa wa marasa galihu da ƙungiyoyi daban-daban, cikinsu har da wasu mutanen daga Dogon Awo da aka ba Naira N500,000 domin kai wani mara lafiya asibiti da kuma wata mata da aka bata Naira 200 domin ta kai ‘yar ta asibiti.

Hon. Hamza Sule ya kuma jagoranci addu’o’i na musamman domin samun ƙarin nasara ga gwamnatin Malam Dikko Umar Raɗɗa da gwamnatin jam’iyyar APC a dukkan matakai.

Sun kuma gudanar da addu’ar samun zaman lafiya da ci gaba mai ɗorewa a yankin Funtua da ɗaukacin Jihar Katsina.

By ukarofi